Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Legas a Ranar Litinin

Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Legas a Ranar Litinin

  • Kotum da ke sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas ta sanar da ranar yanke hukuncinta
  • Kotun ta bayyana ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta kan ƙararrakin da ke gabanta
  • Ƴan takarar jam'iyyun Labour Party da PDP ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun suna ƙalubalantar nasarar da gwamna Sanwo-Olu na APC ya samu

Jihar Legas - Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas na shirin yanke hukunci kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, cewar rahoton PM News.

Ƴan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP), Gbadebo Rhodes-Vivour, da takwaransa na jam'iyyar PDP, Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor sune suka shigar ƙararrakin.

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Legas
Kotun za ta zartar da hukuncinta a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba Hoto: Governor Sanwo-Olu, Rhodes Vivour
Asali: Facebook

Kotun ta bayyana cewa za ta yanke hukuncin na ta ne a ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Shugaban kotun mai shari'a Arum Ashom, shi ne ya sanar da hakan ga dukkanin ɓangarorin a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene dalilin shigar da ƙarar?

Rhodes-Vivour da Jandor suna ƙalubalantar ayyana gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat na Jam’iyyar APC a matsayin waɗanda suka lashe zaben gwamnan Jihar Legas da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi.

Idan ba a manta ba dai a ranar 12 ga watan Agusta, lauyoyin ɓangarorin suka kammala gabatar da bayanansu a gaban kotun.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Sanwo-Olu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Gwamna Sanwo-Olu dai ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye, inda ya doke Rhodes-Vivour na jam'iyyar Labour Party wanda ya zo na biyu.

Gwamnan ya samu ƙuri’u 762,134 inda ya doke Rhodes-Vivour wanda ya samu ƙuri’u 312,329. Jide Adediran (Jandor) na PDP ya zo na uku inda ya samu ƙuri’u 62,449.

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan APC

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Benue, ta tabbatar da nasarar da gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar.

Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Titus Uba suka shigar suna ƙalubalantar nasarar gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng