Oyo: Babban Jigo a Jam'iyyar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Oyo: Babban Jigo a Jam'iyyar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jam’iyyar All Progressives Congress reshen jihar Oyo ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta, Wale Adedibu
  • A cewar rahotanni, Adedibu ya rasu ne sakamakon ƴar gajeruwar jinya a ranar Asabar, 23 ga Satumban 2023
  • Sanata Sharafadeen Alli ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar Adebdibu, inda ya ce rasuwarsa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar shugabar matan jam'iyyar APC a Oyo ta Arewa

Ibadan, jihar Oyo - Allah ya yi wa fitaccen jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Wale Adedibu, rasuwa.

Jigon APC ya rasu a jihar Oyo
Sanata Teslim Folarin ya yi jimamin rasuwar Wale Adedibu Hoto: Teslim Kolawole Folarin
Asali: Facebook

Sanatan APC, jigo sun yi alhinin rasuwar Adedibu

Jam'iyyar APC a jihar Oyo ta bayyana cewa Adedibu ya rasu ne bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya a birnin Ibadan, a ranar Asabar, 23 ga watan Satumban 2023.

Jaridar Nigerian Tribune ta kawo rahoto cewa Sanata Sharafadeen Alli (APC-Oyo ta Kudu), ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da kaɗuwa bisa rasuwar Adedibu.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Legas

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alli ya yi nuni da cewa rasuwar Adedibu na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an yi rashin shugabar matan jam’iyyar APC ta Oyo ta Arewa, a cewar rahoton New Telegraph.

Alli ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga jam'iyyar APC da jihar Oyo, inda rashinsa ya samar da babban giɓi a jihar.

Dan majalisar ya ce rasuwar Adedidu babban rashi ne ga jam’iyyar da kuma jihar, inda ya ce za a riƙa tunawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban siyasa da al'umma.

Shima da yake mayar da martani, Sanata Teslim Folarin ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar Alhaji Adedibu.

Sanarwar da Sanata Folarin ya fitar ta ce:

"Alhaji Wale babban yaya ne, aboki, kuma abokin siyasa, wanda za a yi kewar kyawawan shawarwarinsa da basirarsa ta siyasa"

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Shugabar Matan APC Ta Mutu, Sanata Ya Aike da Saƙon Ta'aziyya

"Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalan mamacin, ƴan jam'iyyar APC da mutanen ƙasar Ibadan."

Shugaban APC Ya Rasu

A wani labarin kuma, an shiga jimami bayan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na wata gunduma a jihar Delta ya rasu.

Shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 9 a karamar hukumar Warri ta Kudu da ke jihar Delta, Mr. Vincent Okokoje ya fadi matacce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel