Tashin Hankali Yayin da Shugaban APC Na Wata Gunduma a Delta Ya Fadi Matacce

Tashin Hankali Yayin da Shugaban APC Na Wata Gunduma a Delta Ya Fadi Matacce

  • Allah ya yiwa wani jigon jam’iyyar APC rasuwa a wani yanayi mai ban tsoro, inda aka ce ya fadi ya mutu nan take
  • Wani abokin aikinsa ya tabbatar da mutuwarsa, inda ya bayyana kadan daga yanayi mai ban takaici da ‘yan APC suka shiga
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan APC ke ci gaba da murnar lashe kujerun siyasa da yawa a kasar nan bayan zabe

Jihar Delta - Shugaban jam’iyyar APC na gunduma ta 9 a karamar hukumar Warri ta Kudu da ke jihar Delta, Mr. Vincent Okokoje ya fadi matacce, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai, takwaransa na gunduma ta 12, Kwamared Gabriel Omorere ya tabbatar da mutuwarsa.

Wannan mutuwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan kammala zabuka a Najeriya tare da sanar da wadanda suka yi nasara.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Yadda jigon APC ya rasu a jihar Delta
Jihar Delta da ke Kudancin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jimamin da ‘yan APC suka shiga a jihar Delta

A cewar Gabriel:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun halarci wani taro tare dashi a gidan wani shugaban APC a Warri ta Kudu, Cif Ojogri a ranar Laraba. Mun samu labarin ya rasu ne a ranar Alhamis da safe.
“Mutuwar Okokoje tashin hankali ne ga APC a Warri ta Kudu da ma jihar Delta baki daya. Marigayi Okokoje mutumin kirki ne da ke son zaman lafiya tsakanin abokansa.”
“Mamacin ya kasance jajirtaccen mutum. Yana daga cikin shugabannin gundunma uku da suka i nasara a zaben da aka kammala kwanan nan a mazabar Warri ta Kudu II.”

Allah ya kawo wani jajirtacce kamarsa

Omorere, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin APC a Warri ta Kudu don mika ta’aziyya ga matarsa, ‘ya’yansa da ilahirin ahalinsa, tabbas jama’a na kusa dashi za su kewarsa, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

Ya kara da cewa:

“Mutuwarsa ta jawo babban gibi a jam’iyyar APC A Warri ta Kudu, ina addu’ar a samu wani irinsa jajirtacce da kuma wanda zai ciyar da jam’iyyar gaba.”

APC ce mafi rinjaye a majalisar dattawa

A wani labarin, kun ji yadda rahoto ya gano cewa, ‘yan APC ne za su fi mamaye majalisar dattawa ta 10 da za a rantsar.

Hakan na zuwa ne a cikin sakamakon zaben da aka kammala kwanan nan na cike gurbi, wanda ya kawo karshen cece-kuce a kasar.

A halin da ake ciki, a watan Yuni ne za a rantsar da majalisa ta 10 da za ta yi aiki tare da Tinubu a wa’adinsa na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel