Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Hyacinth Ali Na Jihar Benue

Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Hyacinth Ali Na Jihar Benue

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Benue ta yi hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC
  • Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jami'iyyar PDP da ɗan takararta Titus Uba suka shigar a gabanta kan nasarar gwamnan a zaɓen 2023
  • Mai shari'ar Ibrahim Ƙaraye ya bayyana cewa kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraronta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Benue - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Benue da ke zamanta a Makurdi, babban birnin jihar, ta tabbatar da nasarar gwamna Hyacinth Alia na jam’iyyar APC.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar Peoples Democratic Party da ɗan takararta na gwamna, Titus Uba, suka shigar, suna kalubalantar zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP a Arewa

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Alia
Kotun zabe ta yi fatali da karar jam'iyyar PDP kan nasarar gwamna Alia Hoto: Fr. Alia TV Network
Asali: Facebook

Kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda ba ta da hurumin sauraron ƙarar, cewar rahoton Channels tv.

Wane dalili ne ya sanya kotun ta yi fatali da ƙarar?

Shugaban kotun mai alƙalai uku, mai shari’a Ibrahim Karaye, ya bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar saboda ƙorafe-ƙorafen da ke cikin ƙarar batutuwa ne da suka shafi gabanin zaɓe kamar yadda sashe na 285 na sabuwar dokar zaɓe ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ta'allaƙa hukuncin na ta ne akan cewa kamata ya yi masu shigar da ƙarar su gabatar da ƙarar rashin cancantar zaɓen Alia da APC ta yi da zargin sanya satifiket ɗin bogi da bayanan ƙarya a fom ɗin EC9 na hukumar INEC kan mataimakinsa, Sam Ode, a gaban kotun ɗaukaka ƙara ba a gaban kotun zaɓe ba

Tun da farko dai, babbar kotun tarayya ta yi fatali da ƙarar ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar PDP kan Hyacinth Alia da mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP

A sakamakon da INEC ta bayyana bayan kammala zaɓen a watan Maris, Alia, wanda limamin cocin Katolika ne, ya samu ƙuri’u 473,933, inda ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa Uba, wanda ya samu ƙuri’u 223,913.

Kotu Ta Tabbatar Na Nasarar Gwamna Mbah

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Enugu, ta tabbatar da nasarar gwamna Peter Mbah na jam'iyyar PDP.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Christopher Agu, ya shigar bisa zargin gwamnan ya yi amfani da takardar shaidar kammala NYSC ta bogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel