Yadda Samari Uku Suka Duka Har Kasa Don Karbarwa Abokinsu Lambar Budurwa a Bidiyo

Yadda Samari Uku Suka Duka Har Kasa Don Karbarwa Abokinsu Lambar Budurwa a Bidiyo

  • Wasu samari uku sun yi amfani da dabara mai ban dariya don samun lambar wayar wata budurwa a bidiyon TikTok da ya yadu
  • Bidiyon na TikTok ya nuno lokacin da samarin uku suka durkusa a kasa sannan suka roki matashiyar yayin da suke neman lambar wayarta
  • Matasan wadanda suka yi magana da Yarbanci, sun jinjinawa budurwar sannan suka sanar da ita cewa abokinsu na ra'ayinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyon TikTok mai ban dariya ya yadu a intanet, inda ya nuno wani dabara mai ban mamaki da wasu matasa uku suka yi amfani da shi don samun lambar wayar wata budurwa da suka hadu da ita a hanya.

Matasan da suka yi magana a Yarbanci sun durkusa a gaban budurwar sannan suka fara yi mata addu'a.

Samarin sun duka a gabanta don nemawa abokinsu lambar wayarta
Yadda Samari Uku Suka Duka Har Kasa Don Karbarwa Abokinsu Lambar Budurwa a Bidiyo Hoto: TikTok/@official_2much
Asali: TikTok

Sun kuma ambaci cewa abokinsu, wanda ke duke a kusa da su, yana sonta kuma yana so ya samu karin bayani a kanta.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Aikewa Saurayi Sakon Rabuwa Bayan Ya Siya Mata Sabon iphone 15, Ya Zauce

Matashiyar wacce ta sanya doguwar abaya mai kyau da mayafi, ta murmusa sannan ta dan dara saboda yanayin yadda suka zo mata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da alama ta ji dadin ta hanyar da suka biyo mata mai ban sha'awa, wanda ke nuna cewa suna iya sace zuciyarta.

Lamarin ya bai wa mutane da dama dariya da sha'awa. Wasu sun jinjinawa matasan kan kwarin gwiwa da tunaninsu, yayin da wasu suka dungi al'ajabin ko yarinyar ta ba su lambar wayar tata.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon samari da ke neman lambar budurwa

Ben Khazzy Fundsya yi martani:

"Suna shirya maki gadar zare sannan kina tsaye kina kallo."

Alarapeboy ya ce:

"An samo wata sabuwar dabara faaa."

Abilawonjoseph77 ya rubuta:

"Ta rigada ta mato."

AyubaToheedAlade:

"Ta rigada ta yarda saboda tana murmushi."

Lola:

Kara karanta wannan

Wata Mai Bukata Ta Musamman Ta Haifi Santalelen Yaro, Ta Nunawa Duniya Shi a Bidiyo

"Za ku gama ku tashi tsaye da subhana robikka."

Bidiyon tagwayen da ke komai tare ya yadu, saurayinsu ma daya

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a sun tofa albarkacin bakunansu a dandalin soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyon wasu tagwaye da ke rayuwa tamkar mutum daya.

Tagwayen suna komai na rayuwarsu a tare kama daga tashi bacci, shiga mota, bandaki harma saurayi guda daya suke da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel