“Tare Muke Wanka Da Bayan Gida, Kuma Saurayinmu Daya”: Tagwayen Da Ke Komai a Tare Sun Magantu

“Tare Muke Wanka Da Bayan Gida, Kuma Saurayinmu Daya”: Tagwayen Da Ke Komai a Tare Sun Magantu

  • Wasu kyawawan tagwaye biyu sun girgiza intanet saboda yadda suke tafiyar da al'amuran rayuwarsu
  • Tagwayen sun ce ji suke tamkar mutum daya ne su lamarin da yasa suke amfani da komai guda daya kama daga waya gado da sauransu
  • Tsananin shakuwa da kusancin da suke da shi, ya sa hatta saurayinsu mutum daya ne

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu a dandalin soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyon wasu tagwaye da ke rayuwa tamkar mutum daya.

Tagwayen suna komai na rayuwarsu a tare kama daga tashi bacci, shiga mota, bandaki harma saurayi guda daya suke da shi.

Tagwaye da ke komai a tare da saurayinsu
“Tare Muke Wanka Da Bayan Gida, Kuma Saurayinmu Daya”: Tagwayen Da Ke Komai a Tare Sun Magantu Hoto: Bristol Live
Asali: UGC

A cikin bidiyon hirar tasu, an jiyo suna cewa:

“Muna tashi daga barci tare, muna wanka tare, muna zuwa bayan gida a tare. A baya mun yi aiki a tare wannan ya yi tasiri. Amma dai mutum daya ake biya cikinmu, kenan dayanmu na aikin sa-kai. Amma dai a kalla muna tare.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna amfani da komai tare, daga mota, wayar hannu, gado, shafin Facebook. Kuma saurayinmu daya.

Da farko na zata zolayata suke yi, Ben ya magantu

Da suka nemi jin ta bakin saurayin game da yadda ya ji a lokacin da suka nemi ya yi soyayya da su a tare sai ya ce:

“Na zata zolaya ce. Na zata kawai so kuke ku ji ta bakina.
“Sun fada mani cewa suna ji kamar su din mutum daya ne. Suna so a dauke su a matsayin mutum daya. Nace zan yi. Zan dauke su tamkar mutum daya, kuma idan sauran mutane suna da matsala da hakan, wannan matsalarsu ce. Kuma bana kallon hakan a matsayin muzgunawa wani.”

Sun bayyana cewa sun shafe kimanin tsawon shekaru 10 kenan da saurayin nasu mai suna Ben kuma cewa mutane da dama sun yi zaton ba za su kai ko’ina ba saboda halin da suke ciki amma sai suka ba marada kunya.

Kara karanta wannan

Bayan Shekara 7 Suna Soyayya, Budurwa Ta Yi Wuff Da Dan Ajinsu, Hotunan Bikinsu Sun Kayatar

Sun bayyana saurayin nasu a matsayin abokin rayuwarsu, makomarsu wanda zai iya yin komai don kyautata masu.

Game da abun da ya hana su yin aure, saurayin ya ce:

“Ina tunanin abun da ke hana mu aure shine hakan haramun ne a kasarmu. Ba za ka iya auren mutum biyu ba. Ina ganin wannan ne babban kalubalenmu. Wanda gaskiya ba ayi mana adalci ba.”

Kan yadda suke kashe kishirwarsu idan bukatuwa ta kama su, sun ce yana kashewa dukkaninsu kishirwarsu, cewa idan ya yi abu da mutum daya a daki sai ya yi wa dayar ma.

Martanin jama'a kan tagwayen da ke rayuwa tamkar mutum daya

@houseofneeyo:

"Saurayinsu ma daya ne."

@JoyUbeku:

"Ka siya daya ka samu daya kyauta "

@Banacubana:

"Kenan saurayi daya suke amfani da shi."

@pelumizpage:

"Baba yana jin dadinsa ya siya biyu a farashin daya."

Kalli bidiyon a kasa:

Matashin da ya siyawa budurwarsa sabon iphone 15 ya zauce bayan ya samu sakon sai wata rana

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Shinkafa ta sauka a Arewa, buhun masara N20,000 a wata jiha

A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya mai suna @graciajoliee a TikTok ta yi fice bayan ta zolayi saurayinta da sakon rabuwa.

Matashiyar ta kadu yayin da saurayin nata ya amsa mata da sakon murna yana mai nuna rudani da takaicinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel