“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini

“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini

  • Wata matashiyar budurwa ta ce maza ba sa sha'awar tunkararta da sunan soyayya kuma cewa bata da saurayi ko daya
  • Matashiyar, Ammie Sweeshy, ta bayyana a TikTok cewa babu wanda ke son soyayya da ita, lamarin da ta alakanta da girman hancin da take da shi
  • Bidiyon da ta wallafa ya nuna cewa hancin Ammie na da girma sosai, kuma tana ta kuka lokacin da aka tambayeta ko tana da saurayi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar budurwa ta koka saboda ta gaza samun saurayi duk da tana burin mallakar guda daya.

Matashiyar ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, Ammie Sweeshy, ta koka sosai cewa babu wanda ke sonta.

Budurwa ta koka saboda rashin saurayi
“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini Hoto: TikTok/@ammie....20.
Asali: TikTok

Matashiyar tana amsa wata tambaya ce da daya daga cikin mabiyanta na TikTok ya yi mata inda ya nemi sanin ko tana da saurayi.

Kara karanta wannan

'Ki Na Da Aljanu Ne?" Bayan Shekaru 2, Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ba Ya Dukanta, Bayanai Sun Fito

"Na so ace ina da guda daya, amma babu mai sona."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon wata budurwa mai katon hanci ya yadu a TikTok

A bidiyon, an gano matashiyar da katon hanci, amma bata bayyana ko da shi aka haifeta ba ko kuma wata lalura ce.

Ammie tana ta kuka cike da dacin rai a bidiyon, cewa ta so ace tana da namiji da za ta kira da sunan nata.

Wasu bidiyoyi a shafinta ya kuma nuno ta tana misali da hancinta. Wasu mutane sun ce duk da haka tana da kyau, duk da katon hancin nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani bayan budurwa ta koka saboda rashin saurayi

@dawgtreyna ta ce:

"Abun dariya kuma hancin ya dace da ke. Duk da haka kina da kyau yariya."

@Princesseron ta yi martani:

"Kada ki damu yar'uwa. Hatta masu karamin hanci, wasu ba su da shi. Don haka naki ma zai zo kuma zai zama na musamman tamkar ke."

Kara karanta wannan

“Diyata Mutum Ce”: Mahaifiyar Kyakkyawar Yarinya Mai Kama Da Yar Tsana Ta Magantu a Bidiyo

@THE FASTEST BAGGER ya ce:

"Kina da kyau kada ki bari abun da mutane ke fadi ya rusaki. Bani da budurwa ko da za ki bukaci saurayi, ki sanar da ni."

Hisbah ta kama mutumin da ya kashe jaririyar da matarsa ta haifa a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa wani magidanci ɗan shekara 28 a duniya da ke zaune a ƙauyen Doka, karamar hukumar Tofa ta jihar Kano, Musbahu Salisu, ya shiga hannun jami'an Hisbah.

Jami'an hukumar 'yan sandan Musulunci ta jihar Kano watau Hisbah sun kama mutumin ne bisa zargin halaka ɗiyarsa mace da matarsa ta haifa kwana ɗaya da haihuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel