Obasanjo Ya Sha Suka Bayan Umartan Sarakunan Gargajiya Su Tashi Tsaye Don Gaishe Da Gwamnan Oyo

Obasanjo Ya Sha Suka Bayan Umartan Sarakunan Gargajiya Su Tashi Tsaye Don Gaishe Da Gwamnan Oyo

  • An yi ta cece-kuce yayin da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya umarci sarakunan gargajiya su tashi tsaye
  • Lamarin ya faru ne yayin wani taro inda Obasanjo ya umarci sarakunan su tashi su gaishe da gwamnan jihar Oyo sannan ya ba su daman zama
  • Mutane sun soki wannan cin mutunci da Obasanjo ya yi wa sarakunan inda su ke ganin rashin gaisuwan ba wata matsala ba ce

Jihar Oyo - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa sarakunan gargajiya tashi tsaye a jihar Oyo.

Obasanjo ya umarci sarakunan su tsaya sannan kuma ya ba ce su daman su zauna bayan sun gaishe da gwamnan jihar, Legit ta tattaro.

Obasanjo ya jawo cece-kuce kan Umartan sarakuna sun gaishe da gwamnan Oyo
Obasanjo Ya Fadi Dalilin Umartan Sarakunan Gargajiya Tashi Tsaye. Hoto: @Oolusegun_obj/@tvcnewsng.
Asali: Facebook

Meye Obasanjo ya umarci sarakunan da yi?

Wannan lamari da ya faru a ranar Juma'a 15 ga watan Satumba yayin kaddamar da ayyuka a Iseyin ya jawo cece-kuce inda aka gayyace shi a matsayin babban bako.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Yafe Masa": Uwargidan Obasanjo Ta Nemi Afuwa Wajen Sarakunan Yarbawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wani faifan bidiyo, an gano Obasanjo na nuna rashin jin dadinshi yadda sarakunan ke zaune ba tare da sun tashi sun gaishe da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ba.

Ya ce wannan rashin da'a ne kuma da cin mutuncin ofishin gwamnan.

Obasanjo cikin harshen Yarbanci ya umarci sarakunan su tashi su gaishe da gwamnan sannan su ka zauna.

Meye mutane ke cewa kan Obasanjo?

Mutane da dama sun soki wannan hali na Obasanjo inda su ka ce wannan rashin da'a da cin zarafi ne ga al'adun Yarbawa.

Oluwo na Iwo, Abdulrosheed Akanbi ya caccaki Obasanjo kan wannan rashin mutunci inda ya ce sarakunan gargajiya sun cancanci mutuntawa.

Akanbi ya ce sarakunan gargajiya sun gaji mulkin ne kuma ya kamata a mutunta su dai-dai gwargwado inda ya soki sarakunan gargajiyan da su ka bi umarnin Obasanjo.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Gwada Shi Da Sarakunan Arewa Ba”: Oluwo Na Iwo Ya Caccaki Obasanjo Kan Umurtan Sarakuanan Oyo Su Tashi

Da aka tuntube shi kan lamarin a ranar Asabar 16 ga watan Satumba, Obasanjo ya fada wa Premium Times cewa ya yi haka ne saboda sun nuna rashin da'a ga gwamna.

Obasanjo Ya Yi Kira Ga Kiristoci Su Shiga Siyasa

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce an lalata zabuka da cin hanci a Najeriya inda ya yi kira ga Kiristoci da su shiga cikin siyasa domin tsaftace ta.

Obasanjo ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, a wajen taron yaye dalibai na shekara-shekara karo na 57 a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel