Matar Obasanjo Ta Nemi Afuwa a Madadin Mijinta Bisa Kunyata Sarakunan Yarbawa

Matar Obasanjo Ta Nemi Afuwa a Madadin Mijinta Bisa Kunyata Sarakunan Yarbawa

  • Uwargidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta roki gafara a madadin mijinta kan kunyata sarakunan Yarbawa da ya yi a jihar Oyo.
  • Taiwo Obasanjo ta ce halin da mijin nata ya nuna a ranar Juma’a, 15 ga watan Satumba, abu ne da ba za a amince da shi ba
  • Ta kuma nemi afuwar sarakunan yankin kudu maso yamma, inda ta roƙi gafara ta dindindin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Taiwo Obasanjo, uwargidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ta roƙi afuwa a madadin mijinta, wanda ya umarci sarakunan Yarbawa da su tashi tsaye yayin wani taro a Iseyin, jihar Oyo a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba.

Taiwo Obasanjo ta miƙa rokonta ga ɗaukacin Yarabawa na duniya, inda ta roƙi samun yafiya ta dindindin mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Gwada Shi Da Sarakunan Arewa Ba”: Oluwo Na Iwo Ya Caccaki Obasanjo Kan Umurtan Sarakuanan Oyo Su Tashi

Uwargidan Obasanjo ta nemi afuwa
Matar Obasanjo ta nemi afuwa a madadin mijinta Hoto: Facebook
Asali: UGC

Ta bayyana cewa abin da mijinta ya aikata bai dace ba a wurin Allah da kuma ƙabilar Yarabawa. Ta ce wulakanta sarakunan ba daidai ba ne kuma cin mutunci ne, rahoton Vanguard ya tabbatar.

"Mijina bai kyauta ba:" Taiwo Obasanjo

A cewar rahoton jaridar Punch, Taiwo Obasanjo ta bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Obasanjo bai kamata ya yiwa sarakunan wulakanci ba domin yi musu gyara, da tona musu asiri cewa suna durƙusa masa a ɓoye. Hakan bai dace ba. Cin mutuncin ya yi yawa."
"Kamata ya yi a yi musu gyaran a keɓe cikin mutunci, ƙauna da girmamawa. Allah ne kawai baya kuskure. Allah maɗaukakin Sarki shi ne sarkin sarakuna."

Ta bayyana cewa sarauta wata cibiya ce da Allah maɗaukakin Sarki ya amince da ita kuma ya kafa ta, kuma dole ba za a ci mutuncinta ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo Na Gab Da Rasa Sarautarsa, An Ba Shi Wa’adi Ya Bai Wa Sarakunan Oyo Hakuri

Wacce irin afuwa ta nema?

A kalamanta:

“Ina son na bayyana a fili cewa a madadin iyalaina, ƴaƴa, matan aure, jikoki da kuma dukkanin ahalin Cif Olusegun Obasanjo, ina bayar da hakuri na gaske na har cikin zuci da zahiri ga dukkanin sarakunan jihar Oyo da dukkanin sarakunan ƙasar Yarbawa da kafatanin ƙabilar Yarbawa da ke a Najeriya da ƙasashen waje."

Obasanjo Ya Fadi Dalilin Umartar Sarakuna Su Mike

A wani labarin kuma, tsohon shugaban Ƙasa, Olusegun Aremu Obasanjo, ya bayyana dalilin da ya sanya ya umarci sarakunan Yarbawa a jihar.Oyo, su miƙe su gaida shi.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda sarakunan sun nuna rashi ɗa'a ga gwamnan jihar, Seyi Makinde.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel