Gaskiyar Lamarin da Ake Ciki Game da Jita-Jitar Juyin Mulki a Kasar Kongo

Gaskiyar Lamarin da Ake Ciki Game da Jita-Jitar Juyin Mulki a Kasar Kongo

  • Rahotanni sun bayyana jita-jitar da ake yadawa a kasar Kongo cewa, an yi juyin mulki tare da hambarar da shugaban kasar
  • Sai dai, a gaskiyar lamari hakan bata faru ba, domin rahotanni sun bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a kasar
  • Ya zuwa yanzu, mun tattaro muku rahoto da ke fitowa daga fadar shugaban kasar tare da jawabi dalla-dalla

Gwamnatin kasar Kongo ta musanta rahotannin yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaba Denis Nguesso na kasar wanda ya shafe shekaru 38 yana mulki.

Wannan na zuwa ne a bayanin Ministan Yada Labarai na Kongo Thierry Moungalla wanda ya wallafa abin da ke faruwa a shafinsa na Twitter.

Batun juyin mulkin Kongo
Batun juyin mulkin Kongo | Hoto: Andy Buchanan - Pool
Asali: Getty Images

A sakon da ya wallafa a kafar yanar gizon kasar, ya ce:

"Bayani mai daukar hankali na nuna wasu manyan abubuwan da ke faruwa a #Brazzaville.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Mutu 2 Tare Da Sace Wasu 3

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Gwamnati ta musanta wannan labarin na karya. Muna ba da tabbaci kan ra'ayin jama'a game da kwanciyar hankali da ke ci gaba da wanzuwa kuma muna rokon mutane da su ci gaba da ayyukansu cikin natsuwa."

Shekara nawa yana mulkin kasar?

Nguesso mai shekaru 78, ya shafe shekaru 38 yana shugabancin kasar da ke Tsakiyar Afirka, kamar yadda ChannelsTv ta ruwaito.

Ya kasance shugaban kasa daga 1979 zuwa 1992, sannan ya dawo a 1997 bayan yakin basasa, kana yake rike da kasar tun daga lokacin zuwa yanzu.

An yi ta samun juyin mulki a fadin Afirka inda a baya-bayan nan aka yi a Gabon da kuma Nijar, inda aka hambarar da shugabannin kasashen.

A nahiyar Afrika ne ake samun shugaban da zai shafe shekaru 30 ko 50 yana mulki, kuma a kan tafarkin demokradiyya mai ikrarin mulkin kama-kama.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Koka, Ya Ce 'Yan Bindiga Sun Mamaye Jiharsa

Jita-jitar Saliyo

A wani labarin, Saliyo kasa ce a Afrika ta Yamma da aka yada labarin yunkurin juyin mulkin da aka ce sojoji da 'yan sanda sun so su yi a cikinta a kwanakin baya.

Labarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattake wuri kan juyin mulkin da sojoji suka gudanar a jamhuriyyar Nijar.

Rahoton da VOA Africa ta yi ya nuna cewa 'yan kasar ta Saliyo sun shiga fargaba biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin 'yan adawa da kuma gwamnatin da ke rike da madafun iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel