Shugaba Tinubu Ya Gana da Shugaban KamfanIn Bua, Za a Karya Farashin Siminti

Shugaba Tinubu Ya Gana da Shugaban KamfanIn Bua, Za a Karya Farashin Siminti

  • Shugaban kamfanin simintin BUA, Abdul-Samad Rabiu ya fara yunkurin karya farashin siminti a Najeriya
  • Ya bayyana shirin da kamfaninsa ke yi na taimaka wa gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa
  • Ya ce kamfanin BUA na ƙoƙarin buɗe sabbin masana'antun siminti nan da ƙarshen shekarar nan 2023

FCT Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Abdul-Samad Rabiu, ya ce kamfaninsa na ƙoƙarin karya farashin siminti a faɗin Najeriya.

Ya bayyana haka ne ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba yayin hira da masu ɗauko rahoto daga fadar shugaban kasa jim kaɗan bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Abdul-Samad Rabiu.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Shugaban KamfanIn Bua, Za a Karya Farashin Siminti Hoto: Abdul-Samad Rabiu
Asali: Facebook

Rabiu ya ce domin tallafa wa kokarin da gwamnati ke yi na sauƙaƙa farashin siminti, kamfanin BUA zai kara masana'antun yin siminti guda biyu a karshen shekara ko farkon shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Kirkiro Sabuwar Ma'aikata Ta Musamman? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

A cewarsa, sabbin masana'antun da ake sa ran shugaba Tinubu zai kaddamar, za su ɗaga adadin simintin BUA zuwa Tan miliyan 17, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban BUA ya ce hakan zai ba kamfanin damar rage farashin simitin zuwa kusan N3,500 kan kowane buhu guda ɗaya.

A kalamansa, Abdul-Samad Rabiu ya ce:

"Bari na fara da gode wa shugaban ƙasa bisa karban bakunci na yau. Na zo ne domin tattauna wa da shi kan harkokin kasuwancin siminti. Muna da sabbin wurare biyu na tan miliyan 3 kowanne wanda zai fara aiki a ƙarshen shekara."
"Saboda haka na zo ne domin gana wa da shugaban ƙasa tare da bayyana masa irin kokarin da muke yi na marawa shirin gwamnati baya domin rage farashin siminti."
“Da wannan tan miliyan 6 da zamu kaddamar a ƙarshen shekara. Kuma mai girma shugaban ƙasa ya amince zai kaddamar da masana'antun, wani lokaci a watan Disamba ko farkon Janairu na shekara mai zuwa."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya, An Faɗi Sunayensu

Farashin da BUA ke kokarin dawo da buhun siminti

Rabiu ya ƙara da bayanin cewa kamfaninsa na kokarin taimaka wa yunkurin gwamnatin Bola Tinubu na rage farashin siminti ta hanyar samar da ƙarin tan 6.

NTA News ta rahoto shugaban BUA na cewa:

"Da zaran mun kaddamar da wadannan wurare biyu kamfanin BUA Cement zai rika samar da kusan tan miliyan 17 a kowace shekara."
"Kuma da wannan ne muka kudiri aniyar sauko da farashin siminti daga N5000 ko N5500 kan kowane buhu a yanzu zuwa ƙila N3000 ko N3500."
“Kuma za mu iya yin hakan ne kawai saboda muna samar da siminti a cikin gida. Kashi 80% na albarkatun da muke amfani da su don samar da siminti suna cikin Najeriya."

Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Ya Musanta Raɗe-Radin Murabus Daga Mukaminsa

A wani rahoton kuma Mista Lucky Aiyedatiwa ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya yi murabus daga matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Najeriya Ta Ƙara Yin Babban Rashi

A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, mataimakin gwamnan ya ce babu wata takardar aje aiki da ya rattaba wa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel