Satifiket: Muhimman Abubuwa 4 Da Jami’ar Chicago Ta Ce Game Da Takardar Ilimin Tinubu

Satifiket: Muhimman Abubuwa 4 Da Jami’ar Chicago Ta Ce Game Da Takardar Ilimin Tinubu

  • Jami'ar jihar Chigaco (CSU) ta jaddada matsayinta cewa Shugaban kasa Tinubu ya kammala karatunsa daga makarantar
  • Sai dai ta bayyana cewa dokar tarayya a Amurka bata ba ta izinin bayyana bayanan dalibai fiye da abin da ta fada a baya ba
  • Sai dai kuma, CSU ta bayyana wasu muhimman abubuwa hudu da zai sa makarantar ta saki shaidar karatun dalibai ga bangare na uku da ya nemi haka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Illinois, Chicago - Jami'ar jihar Chigaco (CSU) ta yi karin haske a kan matsayinta kan takardar shaidar karatun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya nemi wata kotun Amurka ta tilasta a ba shi su.

A wata sanarwa da ta fitar ga CBS News, jami'ar ta lissafa wasu muhimman abubuwa hudu kan takardar shaidar karatun shugaban kasa Tinubu.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Jamai'ar Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Makaranta Bayan Zanga-Zangar Dalibai

Jami'ar Chicago ta magantu kan takardar shaidar karatun Shugaban kasa Bola Tinubu
Badakalar Satifiket: Muhimman Abubuwa 4 Da Jami’ar Chicago Ta Ce Game Da Takardar Ilimin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, muhimman abubuwa guda hudun sun hada da tabbatar da cewa Tinubu ya kammala karatunsa daga jami'ar, sannan cewa dokar kasar Amurka bata ba ta izinin bayyana bayanan karatun dalibai ba sai dai idan da wani dalili.

Ga jerin abubuwan da jami'ar jihar Chicago a kasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Dokar Amurka ta iyakance abun da jami'ar CSU za ta iya bayarwa

Jami'ar jihar Chicago ta jaddada cewar ta kan ba da bayanan dalibai ne idan aka bukata.

Sai dai kuma, ta bayyana cewa dokar kare yancin ilimin iyali da sirri (FERPA) ta kare sirrin bayanan dalibi sannan ta iyakance abin da jami'ar za ta iya bayyanawa ga bangare na uku.

2. Tinubu ya kammala karatu a jami'ar jihar Chicago

CSU ta tabbatar da cewa Shugaban kasa Tinubu ya halarci makarantar kuma ya kammala karatu a 1979 da kwalin digiri.

Kara karanta wannan

Dawowarsa Ke Da Wuya, Tinubu Ya Sake Nada Babban Mukami, An Bayyana Sunanta

Sai dai kuma, jami'ar ta bayyana cewa dokar tarayya a kasar Amurka bata ba ta damar sakin karin bayanai ba tare da amincewar Tinubu ba sai ta hanyar kotu.

3. CSU na da tabbaci kan takardun Tinubu a jami'ar

Jami’ar Jihar Chicago ta bayyana kwarin gwiwarta dangane da bayanan Shugaba Tinubu a makarantar kuma ba ta cikin shari’ar da ake yi da Tinubu a Najeriya.

Sannan ta bayyana cewa za ta saki karin bayani ne kawai bisa umurnin wani alkali na kasar Amurka.

4. CSU ta amsa bukatar bangare na uku

Jami'ar jihar Chicago ta kara da cewar martanin da ta bayar kan bukatar bangare na uku ya yi daidai da ayyukanta, manufofi da dokar tarayya na Amurka.

Ta jaddada cewar za ta ci gaba da yadda take tafiyar da bangare na uku idan ya bukaci bayanan dalibai.

Jami'ar jihar Chicago ta saki takardun shaidar karatun Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa daga ƙarshe jami'ar jiha Chicago ta saki kwafin takardun karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Hadimin shugaban ƙasan kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun shi ne ya sanya kwafin takardun karatun a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel