Bola Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya

Bola Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Aliyu Tijani Ahmed a matsayin sabon shugaban hukumar kula da baƙi da 'yan gudun hijira ta ƙasa
  • Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da wannan naɗi ne a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba
  • Haka zalika shugaba Tinubu ya naɗa shugabar hukumar NSIPA jim kaɗan bayan sauya shugaban hukumar FIRS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Aliyu Tijani Ahmed, a matsayin shugaban hukumar masu neman mafaka, baƙi da 'yan gudun hijira (NCFRMI).

Wannan na ƙunshe ne a wani rahoto da gidan talabin mallakin gwamnatin tarayya NTA News ya wallafa a manhajar X, wadda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamnan PDP Da Tawagar Masu Ruwa da Tsakin Jiharsa a Villa

Shugaba Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin hukumomi.
Bola Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, @NGRPresident
Asali: Twitter

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da naɗin sabon shugaban hukumar NCFRMI a wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar a Abuja.

Ya ce Tijani Ahmed yana da shaidar kammala digiri na ɗaya da na biyu a fannin Sociology kuma ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar Nasarawa a baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika kakakin Tinubu ya ƙara da cewa wanda aka naɗa ya riƙe kwamishinan kananan hukumomi da kwamishinan ilimi duk a jiharsa ta Nasarawa.

A cewar sanarwan, "Bisa umarnin shugaban kasa, wannan naɗin zai fara aiki ne nan take."

Tinubu naɗa shugabar hukumar NSIPA

Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya nada Misis Delu Bulus Yakubu a matsayin shugabar hukumar tsare-tsaren agaji da walwalar al'umma (NSIPA) ta ƙasa.

Sai dai wannan naɗin na Misis Yakubu zai fara aiki ne bayan majalisar dattawan Najeriya ta amince kuma ta tabbatar da ita a muƙamin.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Jimamin Hadarin Jirgin Ruwan Da Ya Janyo Asarar Rayukan Mutane Da Dama a Adamawa

Waɗan nan naɗe-naɗe na zuwa ne jim kaɗan bayan Tinubu ya kori Muhammad Nami daga matsayin shugaban hukumar tattara haraji (FIRS) wanda Buhari ya naɗa.

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna Fubara da Wasu Masu Ruwa da Tsaki a Ribas

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar Ribas karkashin jagorancin gwamna Siminalayi Fubara.

Tawagar masu ruwa da tsakin sun je fadar shugaban kasa ne domin gode wa Tinubu bisa naɗa 'ya'yansu maza da mata a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel