Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Ya Musanta Raɗe-Radin Murabus Daga Mukaminsa

Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Ya Musanta Raɗe-Radin Murabus Daga Mukaminsa

  • Mista Lucky Aiyedatiwa ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya yi murabus daga matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Ondo
  • A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, mataimakin gwamnan ya ce babu wata takardar aje aiki da ya rattaba wa hannu
  • Ya ce shi da mai gidansa gwamna sun yi rantsuwa da Littafi Mai Tsarki cewa zasu kare kundin mulki na tsawon shekaru huɗu

Jihar Ondo - Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Mista Lucky Aiyedatiwa, a ranar Juma’a, ya musanta rattaba hannu kan wata takarda ta ajiye aiki kamar yadda ake yayatawa a wasu bangarori.

Mista Aiyedatiwa ya ce bai san komai ba game da takardar murabus ɗin da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta a baya bayan nan, kamar yadda Punch ta rahoto.

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa.
Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Ya Musanta Raɗe-Radin Murabus Daga Mukaminsa Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa bai yi murabus daga mukaminsa na mutum mai lamba ta biyu a jihar Ondo ba kuma ba shi da niyyar yin hakan.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnan Arewa Ya Zaƙulo Mutane Sama da 100, Ya Naɗa Su Muhimman Muƙamai

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar ranar Juma’a. An yi wa sanarwan take da, "Wasikar murabus da aka riga aka sanya hannu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton The Nation, Mataimakin gwamnan ya ce:

"Ina sanar da cewa ni Lucky Orimisan Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo, ban yi ba kuma bani za niyyar sa hannu a wata takarda ta murabus daga matsayina na zababben mataimakin gwamna."
“Na yi rantsuwa a ranar da aka rantsar da ni tare da Gwamna ranar 24 ga Fabrairu, 2021 don kare kundin tsarin mulkin Najeriya tsawon wa’adin shekaru hudu wanda zai ƙare a ranar 23 ga Fabrairu, 2025."
"Ina nan a mataayina na mai biyayya ga shugabana kuma na tsaya bisa rantsuwar da na yi da Littafi Mai Tsarki na gudanar da cikakken wa'adin shekaru huɗu tare da mai girma Gwamna."

Kara karanta wannan

Kwana 2 Bayan Rantsuwa, Gwamnan APC Ya Tsige Wasu Hadimansa, Ya Naɗa Su a Sabbin Muƙamai

Aiyedatiwa ya aike da saƙo ga al'umma

Ya kuma roƙi mutanen jihar Ondo da majalisar dokokin jihar da sauran 'yan Najeriya baki ɗaya da su yi watsi da irin wadannan jita-jitar “yanzu da kuma nan gaba.”

A farkon makon nan ne aka sallami hadiman mataimakin gwamnan kan harkokin yada labarai daga mukamansu.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna Rotimi Akeredolu, Richard Olatunde ya fitar.

Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Hadimai 136 a Gwamnatinsa

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya amince da naɗa sabbin hadimai 136 a matsayin mambobin majalisar zartarwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ya ce waɗanda aka naɗa sun fito ne daga kananan hukumomin jihar 17.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262