Gaskiya Ana Shan Wahala: Wasu Su na Yin Kwanaki 2 ko 3 Babu Abinci Inji Sarkin Kano

Gaskiya Ana Shan Wahala: Wasu Su na Yin Kwanaki 2 ko 3 Babu Abinci Inji Sarkin Kano

  • Aminu Ado Bayero ya yi jawabi a ranar bikin kanjamau ta Duniya da aka yi a karshen makon nan
  • Sarkin Kano ya yi kira na musamman ga masu wadata da su waiwayi wadanda ke cikin kangin talauci
  • A yayin da yake bayani a Kano, Alhaji Bayero ya bukaci gwamnati ta kawo mafitar matsin rayuwa

Kano - Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga masu hali daga cikin attajiran Najeriya su rika taimakawa marasa hali da ke tare da su.

The Cable ta ce a yammacin Asabar Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi magana da manema labarai domin bikin ranar kanjamau ta duniya.

Sarkin yake cewa akwai gidaje da ake shafe kwanaki biyu zuwa uku ba tare da an samu abin da za a sa a bakin salati ba saboda tsabar talauci.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Sarkin Kano
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a Aso Rock Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

A taimakawa kowa - Sarkin Kano

Alhaji Aminu Bayero ya yi kira ga mawadata su dage wajen taimakawa marasa hali ba tare da la’akari da addini, kabilanci ko addininsu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai martaba ya na ganin cewa taimakawa marasa wadata ne abin da zai kawo zaman lafiya. Kafin nan malamai sun soma wannan kira.

"Ina kira ga attajirai a cikin al’ummun Najeriya su taimakawa masu bukata a cikinsu da ke shan wahala saboda yunwa da halin tattalin arzikin kasar."

- Aminu Ado Bayero

Sarki ya ce wata rana sai labari

Duk da yanayin matsin lambar tattali da tsadar rayuwa da aka samu kai, Sarkin Kano ya bada kwarin-gwiwa cewa ba a haka za a dawwama ba.

Tribune ta rahoto Aminu Bayero ya na mai cewa wata rana za a manta da wannan wahalar da aka shiga na tashin kudin karatu da farashin abinci.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

A lokacin da ake fama da tashin man fetur da tsadar kayan abinci a kasar, Sarkin ya ce masu arziki su rika taimako, su daina jira sai an shiga annoba.

Jikan na Sarki Bayero ya kara da cewa taimako a lokacin annoba bada tallafi na musamman ne, ya ce a yau mutane su na bukatar agaji dare da rana.

"Ba za mu gaza wajen kiranmu ga gwamnati ba yayin da mu ke sanar da ita wahalar da mutanenmu su ke sha.
Mu na kira a gare su da su gano mafitar wahalar da al’ummarmu ke ciki, musamman marasa karfi cikinmu."

- Aminu Ado Bayero

An yi wa Aminu Ado Bayero rashin kunya

Kwanaki mun kawo rahoton wasu matasa da su ka nuna rashin tarbiyyarsu ga Sarki Aminu Ado Bayero, hakan ya jawo 'yan sanda su ka cafke su.

Da aka je bikin sake kaddamar da asibitin Hasiya Bayero, an ji wasu su na ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’, har sai da Gwamna ya tsoma baki tukuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel