Digiri sai Attajiri: Kudin Karatun Jami’a Ya Tashi Ana Tsakiyar Kukan Tsadar Rayuwa

Digiri sai Attajiri: Kudin Karatun Jami’a Ya Tashi Ana Tsakiyar Kukan Tsadar Rayuwa

  • Jami’ar Bayero da ke Kano ta karawa dalibai kudin makaranta, Digiri ya yi tsadar da ba a taba gani ba
  • Amina Umar Abdullahi ta fitar da sanarwar karin kudin bayan taron da shugabannin BUK su ka yi
  • Kudin rajista, kama hayan daki da karbar satifiket bayan gama karatu sun tashi daga shekarar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Jami’ar Bayero da ke garin Kano ta sanar da karin kudin karatu ga masu yin digiri da digirgir, an fahimci cewa farashin ya mummunan tashi.

Legit.ng Hausa ta ci karo da sanarwar da jami’ar ta fitar a makon nan bayan shugabannin makarantar sun yi babban zama na 405 a ranar Litinin.

Sanarwar karin kudin ya fito daga Amina Umar Abdullahi a madadin shugaban jami’ar BUK.

Jami'a
Jami'ar Bayero Kano Hoto: www.buk.edu.ng
Asali: UGC

Karin farashin da aka samu ya yi tasiri a rajista, sayen dakin kwana da makamantansu. Karin ya shafi duk wani matakin karatu da ke jami’ar.

Kara karanta wannan

Sabon Tsarin CBN Zai Jawo Danyen Tashin Farashin Fetur, Lita Zai Iya Haura N580

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda kudin karatu ya koma

Daliban da ke karatu a sashen kiwon lafiya za su fi fuskantar karin kudin makarantar, masu fara digiri a ilmin likita da na hakuri za su biya N170, 000.

Sababbin daliban da za su karanci ilmin jinya a asibiti za su biya N220, 500, akwai bambanci tsakaninsu da tsofaffin dalibai da za su biya N197,500.

A duk shekara, ‘daliban da ke sashen koyarwa za su biya tsakanin N137,500 da N132,500.

Wadanda za su rika biyan mafi karancin kudi (N97, 000) su ne daliban da ke sashen fasaha, ilmin addini da wadanda su ke sashen ilmin zamantakewa.

Sababbin dalibai a bangarorin kimiyya kamar ilmin komfuta za su kashe N100, 000 zuwa N11, 000.

Abin bai tsaya nan ba, sai an biya N150, 000 a matsayin kudin fam kafin a iya canza jami’a, idan ana son karbar takardar shaida karatu za a biya N12, 000.

Kara karanta wannan

Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

Ga masu neman daki kuwa, za su kashe N37, 590 zuwa N80, 090 daga shekarar bana. Abin da ya kawo bambancin shi ne samun katifa a cikin dakin kwanan.

Menene ya jawo haka?

Dr. Kabir Danladi Lawanti malami ne a jami’ar ABU Zariya, ya fada mana ya zama dole a kara kudin makaranta domin an tsuke bakunan aljihunsu.

"Lamarin ya yi kamari daga 2016 a karkashin Muhammadu Buhari, gwamnatinsa ce ta fi yi wa harkar ilmi rikon sakainar kashi bayan dawowa mulkin farar hula.
Hakan ya jawo aka yi ta zuwa yajin-aiki a mulkinsa, musamman ‘yan kungiyar ASUU. Gwamnatinsa tayi wa ma’aikata horo da yunwa domin ganin ta taka masa burki.
Iyaye da dalibai sun goyi bayan wannan mataki, a karshe jami’o’i su ka kara kudi domin babu yadda su ka iya. A karon kan ta, ASUU ba ta goyon bayan yin hakan."

- Dr. Kabir Danladi Lawanti

Fetur zai kara tsada?

Kara karanta wannan

“Ya Fi Karfin Talaka”: Jami’ar Najeriya Ta Kara Kudin Makaranta Da Kaso 300, Dalibai Sun Yi Martani

A wurare da-dama, man fetur ya kai N540, yanzu labari ya zo cewa kudin ya fara wuce hakan a wasu garuruwa saboda karyewar Naira a kasuwar canji.

Matakin da bankin CBN ya dauka ya yi sanadiyyar canza farashin da ake shigo da man fetur daga kasashen waje. Bayan nan an ji motoci za su kara tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel