An Cafke Masu Yi Wa Sarkin Kano Rashin Kunyar ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’

An Cafke Masu Yi Wa Sarkin Kano Rashin Kunyar ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’

  • Akwai wadanda su ke da burin a canza Sarkin Kano bayan canjin gwamnati da aka yi a Jihar
  • A wajen bude asibitin Hasiya Bayero aka ji wasu matasa su na ta ihun a tsige Aminu Ado Bayero
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya shaida cewa sun yi amfani da fasahar zamani, ana cafke marasa da’ar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Kano ta bada sanarwar neman mutanen da su ka yi wa Alhaji Aminu Ado Bayero ihu na rashin da’a.

The Nation ta ce Kwamishinan ‘yan sanda, CP Muhammad Gumel ya bayyana haka yayin da ya kira taron manema labarai jiya a garin na Kano.

A ranar Lahadi, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya je kaddamar da asibitin Hasiya Bayero, aka samu wasu da su ka yi masa rashin kunya.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

Sarkin Kano
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

An sake bude asibitin Hasiya Bayero

CP Muhammad Gumel ya ce wadanda ake zargi sun jawo hayaniya yayin da ake sake bude asibitin yara na Hasiya Bayero da ke kusa da fadar Sarki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan ya ce masu zanga-zangar sun fito cikin bainar jama’a, su na sakin kalaman da ake ganin cin mutunci ne ga Mai martaba Sarki.

An ji tsagerun su na kiran ‘Sabon Gwamna, sabon Sarki’, su na masu kira ga sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tunbuke Aminu Ado Bayero.

A 'yan kwanakin nan, wasu su na kiran a maida Muhammadu Sanusi II kan karaga.

Za mu cafko wadanda su ka rage - CP

Gumel ya ce ‘yan sanda sun yi amfani da fasahar zamanin yau wajen cafko wasu daga cikin marasa da’ar, kuma ana cigaba da neman ragowar.

Kara karanta wannan

Akpabio ya Shiga Uku, Sanatan APC Ya Fallasa Kudin Hutun da Ake Rabawa Tun 1999

The cable ta ce baya ga wadanda aka kama, ‘yan sanda za su yi kokarin binciko masu daukar nauyinsu domin ba za a bari a ci mutuncin sarauta ba.

"Ba a gayyaci mutanen nan zuwa wajen taron ba, sai dai sun kutso ne kurum a karon kansu.
Dole akwai wasu mutane ko kungiyar da ta ke daure masa gindi, an iya gano mutane shida.
Mun yi amfani amfani da fasaha domin yin ram da su, mu na cigaba da nazarin faifen bidiyon, kuma mu na kokarin cafke duk masu hannu."

CP Muhammad Gumel

Mulki na Allah SWT ne

Mubarak Bashir mazaunin Kano kuma masoyin Mai martaba Aminu Ado Bayero, ya shaida mana cewa bai kamata a rika cusa siyasa a harkar sarauta ba.

Da ya yi magana da Legit Hausa, matashin ya bada shawarar a darajar gidan sarauta.

"Ya kamata mutane su ajiye siyasa a gefe su rika ganin mutuncin sarakunanmu, su daina bari yan siyasa suna amfani da su don cima wata manufa ta su.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

Mutane su yadda mulki Allah ne yake karbewa ga wanda yaso ya bawa wanda yaso babu abinda wani Dan Adam ya isa ya yi, komai na Allah (SWT) ne."

- Mubarak Bashir

Kwanaki 100 a ofis a Kano

Kwanaki kun ji labari Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar duba aikin babban titin Wuju-Wuju da yake so a kammala a Satumba.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na so ta samu ayyukan da za ta kaddamar zuwa lokacin da za tayi bikin cika kwanaki 100 a karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel