Dan Damfara Na Farautar Malamin Addini Kan Addu’ar Bogi A Jihar Ogun

Dan Damfara Na Farautar Malamin Addini Kan Addu’ar Bogi A Jihar Ogun

  • Malamin addinin Musulunci ya shiga masifa yayin da dan damfara ke namansa ruwa a jallo
  • Malamin mai suna Sulaimon ya yi wa dan damfarar ne addu’a don samun nasara amma ba ta yi ba
  • Dan uwan malamin da ake nema, Hamzat ya bayyana yadda abin ya faru da kuma halin da ake ciki

Jihar Ogun - An ruwaito cewa wani dan damfara ta yanar gizo ya dauki hayan soja don farautar wani malamin addinin Musulunci mai suna Sulaimon a jihar Ogun.

Dan damfarar da ba a bayyana sunansa ba, na zargin malamin addinin da masa addu’a amma bai samu abin da ya ke nema ba a harkokinsa.

Malamin addini ya tsere bayan addu'ar bogi wa dan damfara
Rundunar 'Yan Sanda Ta Fara Bincike Kan Lamarin. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye dan uwan malamin ke cewa?

Mafi yawan ‘yan damfara na neman taimakon malaman addinai daban-daban da masu ba da maganin gargajiya da matsafa don cimma burinsu.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ke magana da ‘yan jaridu, dan uwan malamin mai suna Hamzat ya ce sojoji sun zo sun mamayi gidan bulok dinshi a unguwar Bankole da ke karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar.

Ya ce yayin mamayar, sojojin sun tafi da motarsa kirar Toyota RAV 4 inda ya ce shi ne ya hada dan damfarar da dan uwansa don taimaka masa da addu’o’i.

Ya bayyana dalilin neman malamin

Hamzat, yayin da ya ke bayyana abin da ya faru, ya ce:

“A ranar Talata an kira ni cewar wasu sun zo gidan bulok dina za su sayi kaya, na yi sauri na dawo kawai sai naga sojoji su na kokarin kama ni.
“Da na duba cikin mota sai na ga yaron da na hada da dan uwana da kanwarsa wacce budurwata ce.

Kara karanta wannan

Tsabagen Kiyayya Ya Jawo Mawaki Ya na Kiran Sojoji Su yi wa Tinubu Juyin Mulki

“Sojojin sun bukaci in ba su motata amma naki na ce zan tuka motata in bisu tun da ba sata na yi ba kuma ban aikata wani laifi ba.”

Ya kara da cewa Naira dubu 10 ce ta raba su amma da sharadin cewa idan bai kawo dan uwansa, Sulaimon ba za su sake kama shi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Omotola Odutola ta tabbatar da hakan inda ta ce yanzu haka ana kan bincike a kan lamarin.

Jami'an Tsaro Sun Kama Matashi Kan Kisan Mahaifinsa A Ogun

A wani labarin, An kama wani matashi mai shekaru 20 a jihar Ogun kan kisan mahaifinsa saboda kudin asiri.

Wanda ake zargin mai suna Ridwan an kama shi ne a kauyen Oshoku da ke karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel