Hukumar DSS Ta Tsare Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamnan APC Da Karkatar Da Kudade

Hukumar DSS Ta Tsare Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamnan APC Da Karkatar Da Kudade

  • Hukumar DSS ta garkame dakataccen shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas ta jihar Ogun, Wale Adedayo
  • Adedayo dai ya zargi Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun da karkatar da kudaden kananan hukumomi lamarin da ya kai ga dakatar da shi
  • An tattaro cewa dakataccen shugaban karamar hukumar ya amsa gayyatar da hukumar tsaron farin kaya ta yi masa a ranar Juma'a amma sai ta tsare shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta tsare dakataccen shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, kan zargin da ya yi wa Gwamna Dapo Abiodun da badakalar kudade.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an hukumar DSS reshen jihar Ogun ne suka tsare Adedayo a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Sauya Wakilan Ondo da Cross River a Hukumar NDDC, Cikakken Bayani

DSS ta tsare shugaban karamar hukuma da ya zargi gwamnan Ogun da karkatar da kudade
Hukumar DSS Ta Tsare Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamnan APC Da Karkatar Da Kudade Hoto: Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Adedayo ya zargi gwamnan da rike kudaden kananan hukumomi tsawon shekaru biyu da suka gabata.

An tattaro cewa Adedayo ya je ofishin DSS da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Juma'a domin amsa gayyatar da suka yi masa kan zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abiodun ya ziyarci ofishin DSS

Ya kuma ziyarci ofishin DSS a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta kan wannan lamari, amma sai a ranar Juma'a ne suka tsare shi.

Daya daga cikin hadimansa ya sanar da jaridar Daily Trust a daren ranar Juma'a cewa akwai yiwuwar Adedayo ya shafe hutun karshen mako a tsare.

Ya ce:

"Mun iso nan tare sannan na karbi wayara na kuma tsaya a waje, tun daga lokacin ba a bari ya fito waje ba.
"Bayan ya isa cikin wajen, gwamnan ma ya zo ofishin DSS sannan ya tafi bayan kimanin mintuna 30. Allah kadai ya san abun da ke faruwa da ubangidana a yanzu, don Allah ku taimaka mana, karfe 8:34 na dare ya yi kuma har yanzu ba bar shi ya fito waje ba."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS Ta Kama Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Obiora

An dakatar da shugaban karamar hukuma da ya zargi Gwamna Abiodun da badakalar kudi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rikici ya kunno kai a jihar Ogun, yayin da kansiloli suka dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, wanda ya zargi gwamnan jihar Dapo Abiodun da baɗaƙalar kuɗaɗe.

Da safiyar Alhamis ne jami'an tsaro ɗauke da makamai tare da wasu 'yan daba sun kutsa kai sakatariyar ƙaramar hukumar da ke Ogbere duk a cikin yunƙurin tsige shugaban kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel