Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

- Ƴan sanda a Jihar Kano sun cafke wata matar aure da ake zargi da antayawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi

- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da hakan

- Mahaifiyar wadda aka ƙona da ruwan zafin, Hajiya Binta Ismail tana roƙon gwamnati da masu hannu da shunni su taimaka musu da kuɗin magani

Rundunar yan sandan Jihar Kano, ranar Litinin, ta kama wata mata mai shekara 30, Hauwa Auwal a unguwar Shekara Sabuwar Abuja a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar, bisa zargin shekawa kishiyarta Sha'awanatu Muhammad da yarta mai shekara hudu, Halima Khalid, ruwan zafi.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, The Punch ta ruwaito.

Wata mata ta sheƙawa kishiyarta ruwan zafi a Kano
Wata mata ta sheƙawa kishiyarta ruwan zafi a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja (Hotuna)

Ya ce jami'an yan sanda sun dira gidan bayan sun samu rahoton afkuwar lamarin tare da kama mai laifin hadi da garzaya wa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da wanda abin ya shafa don yi musu magani.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa

A nata bangaren, mahaifiyar mai jinyar, Hajiya Binta Ismail ta roki gwamnatin Jihar da sauran masu hali da su taimaka su biya kudin maganin yar ta da jikar ta.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel