Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana

Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana

A ranar Juma’a ne wata kotun majistri dake zamanta a Ile-Ife, a jahar Osun ta saurari karar da aka shigar da wani Magidanci, Akinde Adeniyi dan shekara 27 bisa cin zarafin matarsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito ana tuhumar Adeniyi da watsa ma matarsa Deborah tafasashshen ruwan zafi ne sakamakon zarginta da yake yi da cin amana ta hanyar bin wani saurayi.

KU KARANTA: Alkalin da ya soke zaben Abiola na ranar June 12 1993 ya rasu a Bauchi

Dansanda mai shigar da kara, Ona Glory ta bayyana ma kotun cewa mijin ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Afrilu a unguwar Modakeke-Ife, kuma ya zuba yaji a cikin ruwan zafin.

Sai dai ko da aka karanta masa tuhumar da ake masa, sai Adeniyi ya tsaya kai da fata atafau bai aikata wannan mummunan laifi da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana
Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Daga nan sai Alkalin kotun, Mai Sharia Joseph Owolawi ya bayar da belin mutumin a kan kudi N100,000 da mutum guda da zai tsaya masa a kan N100,000.

Bayan nan sai Alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya nada sabbin alkalai guda hudu na kotunan jahar Katsina a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Alkalan da aka nada sun hada da Safiya Badamasi Umar SAN da Barrister Ashiru Sani a matsayin Alkalan babbar kotun jahar.

Sai kuma Mohammad Makiyyu Adam da Adam Salihu Yarima a matsayin Alkalan kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci.

Masari ya bayyana musu cewa nadin nasu na tattare da hakkoki masu nauyi a wuyansu dake bukatar kwarewa da sadaukar da kai wajen sauke su, tare da tsoron Allah wanda shi ne a gaba.

“Bangaren sharia na fuskantar kalubale da dama a wannan lokaci, daga ciki har da jan kafa da ake samu wajen kammala shari’u, don haka akwai bukatar yi ma tsarin garambawul don tabbatar da samar da adalci a jahar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng