Mutumi Ya Aika Hoton Tsohuwar Buduwarsa Tsirara ga Sabon Mai Shirin Aurenta

Mutumi Ya Aika Hoton Tsohuwar Buduwarsa Tsirara ga Sabon Mai Shirin Aurenta

  • ‘Yan sanda sun tabbatar da cafke wani saurayi da yake neman bata shirin auren tsohuwar buduwarsa
  • Da ya ji labari sahibarsa za ta yi aure, sai Osayande Efosa ya aika hoton batsa ga mai neman auren na ta
  • Ogechi Nwokolo ta sanar da ‘yan sanda abin da ya faru, yanzu maganar ta kai ga ‘yan sanda, za a je kotu

Abuja - Jami’an ‘yan sandan jihar Edo sun cafke mai shekara 31 bisa zargin aikawa manemin auren tsohuwar budurwarsa hotunanta tsirara.

Abin da ya faru kamar yadda Daily Trust ta rahoto shi ne, wata Ogechi Nwokolo ta sanar da jami’an tsaro abin da yake faruwa a garin Benin.

Miss Nwokolo ta hada matashin da sashen ‘yan sanda da ke yaki da ‘yan damfarar yanar gizo da masu garkuwa da mutane na reshen jihar Edo.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Abba Gida-Gida Ya Lashi Takwabin Aurar Da 'Yar Da TikTok Murja Kunya

Tsirara
Hoton mace tsirara a Brazil Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan sanda sun cafke Efosa

Kwamishinan ‘yan sanda, Muhammed Dankwara yake cewa wanda abin ya shafa ta ce tsohon saurayinta, Osayande Efosa ya yi mata lalata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwar ta zargi Mista Osayande Efosa da aika hotunta tsirara ga wani Bawan Allah wanda ta ke shirin tarewa da shi a matsayin mijin aure.

"In kashe ki idan ki ka fadawa 'yan sanda"

Ba a nan saurayin ya tsaya ba, ya yi wa tsohuwar masoyiyarsa barazanar zai hallaka ta muddin ta sanar da jami’an ‘yan sanda halin da ake ciki.

Rahoton ya ce CP Muhammed Dankwara ya shaida cewa wanda ake zargi ya amsa laifinsa da bakinsa, kuma za su mika shi kotu ayi shari’a.

Efosa: Ta na shirin auren wani

Da aka zanta da shi, tsohon saurayin na Ogechi Nwokolo ya fadawa manema labarai cewa sun shafe fiye da shekara guda su na soyayyarsu.

Kara karanta wannan

Kaico: Akalla mutum 61 aka mayar marayu bayan harin da aka kai masallacin Kaduna

Sai rana kwatsam ya ji za ta auri wani dabam, alhali ta yi masa alkawarin za ta zama matarsa, da alama dai daga nan ne kishinsa ya motsa.

Abin da hakan ya ke nufi a wajen matashin shi ne an ci amanarsa, sai dai ya ce bai da wata muguwar manufa kamar yadda wasu ke tunani.

An tare motoci a titin Abuja-Lokoja

Ana da labari kwanan nan an tare wasu motoci da karfe 7:30 na dare, dole direbobi su ka hakura da tafiya da ‘yan bindigan su ka harbe tayoyinsu.

Motocin na tsayawa sai ga wasu mutane dauke da bindigogi, su ka ingiza su cikin jeji. Abin ya faru ne a kan hanyar nan Abuja zuwa Lokoja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel