Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

  • Yunkurin da wata budurwa yar Najeriya ta yi na shiga kundin bajinta na Guinness ya shafi soyayyarta domin dai saurayinta ya fasa aurenta
  • A cewar budurwar wacce ta shiga gasar zaman cikin gida na awanni 168, ya ce wai ta kunyata shi a soshiyal midiya
  • Batun janye auren da saurayinta ya yi ya haifar da cece-kuce yayin da mutane suka caccake ta

Funmi Ojelade, wata matashiya yar Najeriya wacce ta sanar da cewa za ta shiga gasar zaman gida na awanni 168 yan makonni da suka gabata don shiga kundin bajinta na Guinness ta koka cewa saurayinta ya rabu da ita.

Funmi ta ce ya kwace zoben alkawarin aure da ya bata, cewa ta kunyata shi da rokon data da ta yi a soshiyal midiya.

Saurayinta ya rabu da ita saboda tana son kafa tarihi a duniya
Yadda Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Duniya, Ya Ce Ta Kunyata Shi Hoto: TikTok/ @x_taclie
Asali: TikTok

Ku tuna cewa Funmi, wacce ta fara gasar zaman gidanta a ranar 15 ga watan Yuli, ta roki jama’a a yan makonni da suka gabata, cewa ta karar da datan 2.5GB da ta siya.

Kara karanta wannan

Malamar Makaranta Ta Sharbawa Daliba Zane 4 a Fuska, Mahaifiyar Yarinyar Ta Saki Hotuna

Da take bayyana labaran da wasu shafukan labarai suka yi daga gasar zaman gidanta, Funmi ta koka cewa an yi watsi da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Me yasa sai ni ku taya ni rokonsa faaaa,” ta rubuta yayin da take rokon jama’a.

Ta sha suka sosai a kan wallafar da ta yi, inda wasu suka kira ta da mai neman suna.

Lamarin Funmi Ojelade ya haddasa cece-kuce

doxy ta ce:

“Baaba mutane na da taurin zuciya da suke wallafa duk abun da ke damunsu ki zo a karshe ki aure mijinki sannan ki zo ki ga wallafar da kika yi a baya.”

THRIFTBYTIFE ta ce:

“Jinjina ga dangina na kusa da nesa…ku din manyan mutane ne…Ka ji fa sai ku yi ta kunyata kanku a duniya.”

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Hakura Da Biliyan 300 Da Za Ta Gada Don Auren Masoyinta Bakin Fata, Iyayenta Sun Yafewa Duniya Ita

Asher Great ta ce:

“Kamar dai Dammy, wannan ba neman suna mai kyau bane.”

Lucid ta ce:

“Kina so ki kafa tarihi amma sai kika karya zuciyarki da kanki.”

Malamar makaranta ta sharbawa dalibarta zane hudu a fuska

A wani labari na daban, mun ji cewa wata uwa ta ce wata malamar makaranta ta sharbawa diyarta zane guda hudu a fuska ba tare da izini ba.

Wani hoton yarinyar da shafin gidan radiyon Ilorin, Sobi Fm, ya wallafa a Facebook ya nuno yarinyar dauke da zane hudu a gefen kuncinta na dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel