"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Juna Biyu Ba Tare Da Kwanciyar Aure": Matar Aure Ta Gaya Wa Kotu

"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Juna Biyu Ba Tare Da Kwanciyar Aure": Matar Aure Ta Gaya Wa Kotu

  • Wata matar aure mai neman saki a gaban kotu tace ba za ta iya yin bayanin yadda aka yi ta samu juna biyu
  • Matar ta gayawa kotu cewa duk da ba su yi kwanciyar aure da mijinta ba, amma sai ga juna biyu ya bayyana a tare da ita
  • Mijin nata ya musanta kalaman da ta yi a gaban kotun inda ya ce sun raya Sunnah da matarsa akan gado

Jihar Kwara - Wata mata mai neman saki a gaban kotu, Taibat Abubakar, ta gaya wa kotun majistare mai zamanta a Ipata cikin birnin Ilorin na jihar Kwara, cewa ba ta san yadda aka yi ta samu juna biyu ba.

Taibat ta bayyana cewa ba za ta iya yin bayanin yadda ta samu juna biyu ba tun da ba ta yi kwanciyar aure ba da mijinta, Mr Salihu Abubakar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Ta Ki Bari Su Raya Sunnah

Matar aure na neman saki a gaban kotu
Matar auren tace ba su yi kwanciyar aure da mijin ba amma an samu juna biyu Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A kalamanta:

"Ya ce na aure shi amma na ce aa saboda bana son shi. Amma ya nace inda ya ce sai na aure shi ko ina so ko ba na so."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kwatsam kawai wata rana sai ya kirani yake cemin ina ɗauki da juna biyunsa kuma kada na kuskura na zubar da shi. Duk da na yi mamaki amma ban ɗauki abun da gaske ba har sai da na ga jinin al'ada ta bai zo ba a ƙarshen wata duk da cewa ba mu yi kwanciyar aure da shi ba."
"Ya biya kuɗin sadakina kuma na haifar masa yaro ɗaya, amma yanzu ban ƙaunar shi kwata-kwata."

Taibat, wacce ta nemi kotun da ta raba aurensu, ta buƙaci ya riƙa biyanta kuɗin ciyar da yaron N10,000 duk wata, sannan ta kuma kotun da ta sanya mijin na ta ya riƙa biyan kuɗin makarantar yaron.

Kara karanta wannan

“Ya Fi Kudin Jini”: Budurwa Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2, Ta Ce Mahaifiyar Tata Za Ta Fahimce Ta

Mijin ya musanta bayanin da matarsa ta yi a gaban kotu

Salihu ya musanta bayanan da Taibat, inda ya ce da farko ba ta karɓi tayin da ya zo mata da shi ba amma daga baya sun daidaita kansu.

"Mun yi kwanciyar aure da ita cikin hankalinmu ba a cikin mafarki ba ko sihiri kamar yadda ta ke cewa." A cewarsa..

Majistare Ajibade Lawal, ta gayawa ma'auratan cewa su tsaya a yadda su ke har sai zuwa ranar da za a cigaba da sauraron shari'ar ta 25 ga watan Yulin 2025.

Magidanci Na Son Kotu Ta Raba Aurensa Da Matarsa Saboda Duka

A wani labarin kuma, wani magidanci ya garzaya kotu neman ya datse igiyar aurensa da matarsa saboda tana haɗa baki da saurayinta ya lakaɗa masa dukan tsiya.

Sai dai kotun ta gano duk da kwashe shekara 22 a tare babu aure a tsakaninsu inda ta yi ƙarin haske kan dalilin aukuwar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel