Matar Aure A Abuja Ta Fashe Da Kuka Yayin Da Mai Tura Baro Ya Tsere Da Kayan Abinci Da Ta Siya

Matar Aure A Abuja Ta Fashe Da Kuka Yayin Da Mai Tura Baro Ya Tsere Da Kayan Abinci Da Ta Siya

  • Wata mata ta shiga yanayin kunci bayan wani dan dako ya tsere mata da kayan abinci da ya kai Naira dubu 23
  • Matar mai suna Rebecca Gbaje ta ce ta zo kasuwar Kwaita ne daga Fogbe don siyan kayan a kasuwa da ke Kwali a birnin Abuja
  • Jama'a sun bazama neman dan dakon ko za a dace, yayin daga bisani su ka yi wa matar karo-karo na wasu kudade don siyan wani kayan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wata matar aure ta fashe da kuka bayan dan dako ya tsere mata da kayan da ta siya a kauyen Kwaita da ke Kwali a birnin Abuja.

Matar mai suna Rebecca Gbaje ta shiga wani yanayi inda mutane da dama a kasuwar su ka taru su na mata jaje ganin yadda abinci ke tsada.

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Gina Makeken Gida Harda Ramin Wanka Na Musamman, Ya Hadu Matuka

Mai tura baro ya gudu da kayan wata mata a Abuja
Mai Tura Baron Da Ya Tsere Da Kayan Matar Aure A Abuja. Hoto: Tori News.
Asali: Facebook

Meye aka sace wa matar a kasuwar?

Har ila yau, mutane sun bazama neman dan dakon ko za a dace wurin kamo shi, Tori News ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ta ke mai da martani, matar ta ce ta sayi shinkafa da wake da masara da sauran kayayyaki inda ta bukaci dan dakon ya kai mata bakin titi.

Bayan sun fara tafiya ne ta tsaya don siyan kifi inda ta bukaci ya jira ta, daga nan ne fa ba ta sake ganin shi ba, sama ko kasa.

A cewarta:

"Bayan na gama siyan kifin, na nemi dan dakon ban gan shi ba ko sama ko kasa."

Wani taimako matar ta samu daga mutane?

Matar ta ce ta zo ne daga kauyen Fogbe da ke birnin zuwa kasuwar Kwaita don siyan kayan da su ka kai har Naira dubu 23.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: Halin Kunci Ya Jefa Magidanta Cikin Yanayi Inda Su Ke Satar Kayan Gona Don Ci Da Iyali

Daily Trust ta tattaro cewa mutane da dama sun harhada mata kudade don siyan wani kayan bayan ta gagara yin shiru da kukan da ta ke yi a kasuwar.

Matan Aure Sun Yi Zanga-zanga A Kaduna

A wani labarin, matan aure sun yi zanga-zangar lumana a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a cikin jihar Kaduna don nuna damuwarsu da halin da ake ciki.

Matan sun yi zanga-zangar ne don nuna damuwa da kuma tsadar kayayyaki a kasar inda su ka roki Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel