Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Gina Makeken Gida Harda Ramin Wanka Na Musamman, Ya Hadu Matuka

Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Gina Makeken Gida Harda Ramin Wanka Na Musamman, Ya Hadu Matuka

  • Wata budurwa yar Najeriya mai tsananin wayo ta zuba jari da kudinta inda ta ginawa kanta hadadden gida tana da shekaru 20
  • Mutane da ke shakkar cewa gidanta ne sun ga karin bidiyoyinta tana magana tare da kewaya cikin gidan
  • Matasan yan Najeriya sun garzaya sashinta na sharhi domin nuna mamakinsu a kan dankareren gidan ta ginawa kanta

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta cimma muradionta na gina gida da zama mai gidan kanta tun tana da kuruciyarta.

Matashiyar ta dauki hoto a gaban gidan da aka kammala gininsa tare da iyayenta yayin da ta kasance rike da takardun gidan.

Budurwa ta kera gida mai kyau
Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Gina Makeken Gida Harda Ramin Wanka Na Musamman, Ya Hadu Matuka Hoto: @everythinglabam0
Asali: TikTok

Budurwa ta kera gida da ramin wanka

Wani bidiyon TikTok da kanwarta @everythinglabam0 ta wallafa, an gano matashiyar tana zagaya cikin harabar gidan don nuna jin dadinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yadda Juna Biyu Ya Sauya Kyakkyawar Budurwa Ta Zama Wata Daban, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yayin da wasu mutane suka nuna shakku a kanta, @everythinglabam0 ta saki wani bidiyo don tabbatar da cewar ta mallaki gida a shekaru 20.

Jama'a da suka ga karin hujja na bidiyon sun garzaya sashinta na sharhi domin taya ta murnar wannan nasar. Sun yi fatan samun irin wannan nasara.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon yar shekaru 20 da ta dankara gida

margaretama216 ta ce:

"Ina taya ki murna yar uwa akalla dai baki yi amfani da kudin kin siya gashi yan kanti ba na taya ki murna."

Bianca Sweetlife ta ce:

"Na taya ki murna Allah ya yi mun irin taki."

user7866673228255 ya nuna shakku:

"Sabon zolaya don Allah."

Tasha banks ta ce:

"Na taya ki murna yar'uwa, zai kai hannunmu muma."

Juliet Obasuyi ta ce:

"Na taya ki murna yar'uwa."

ivoryakwari993 ta ce:

"Na taya ki murna yar'uwa Allah ya yi mun ya taki."

Kara karanta wannan

Yadda Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

Jessy wealth ta ce:

"Don Allah masoyiya ki bibiyeni sannan ki yi karin bayani, na taya ki murna yar'uwa."

Saurayi ya rabu da budurwarsa saboda shiga kundin bajinta na Guinness

A wani labari na daban, mun ji cewa Funmi Ojelade, wata matashiya yar Najeriya wacce ta sanar da cewa za ta shiga gasar zaman gida na awanni 168 yan makonni da suka gabata don shiga kundin bajinta na Guinness ta koka cewa saurayinta ya rabu da ita.

Funmi ta ce ya kwace zoben alkawarin aure da ya bata, cewa ta kunyata shi da rokon data da ta yi a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel