Bidiyon Yadda Dan Adaidaita Ya Jera Tankunan Ruwa 13 a Kan Keke Ya Dauka Hankali

Bidiyon Yadda Dan Adaidaita Ya Jera Tankunan Ruwa 13 a Kan Keke Ya Dauka Hankali

  • Wani mai tukin adaidaita a Najeriya ya loda tankunan ruwa 13 a saman kekensa, amma ya sha gwagwarmaya wajen buka shi a hanya mai gargada
  • An daura tankokin kan juna sannan aka daure su da igiya a saman adaidaitan, inda ya kewaye jikin karamin keken
  • Masu amfani da Twitter da dama da suka ga bidiyon sun ce dan adaidaitan ya yi kasada sosai da yawan tankunan da ya dauka

Wani mai tukin adaidaita ya yi gagarumin kasada ta hanyar loda manyan tankunan ruwa guda 13 a zaman kekensa.

Bidiyon mutumin yana gwagwarmayar tuka adaidaita sahun a unguwanni ya yadu a dandanin Twitter.

Dan adaidaita ya yi lodin da ya fi karfinsa
Bidiyon Yadda Dan Adaidaita Ya Jera Tankunan Ruwa 13 a Kan Keke Ya Dauka Hankali Hoto: Twitter/@gistlover.
Asali: Twitter

Ta kai har manyan tankunan sun kusa shan kan Keken yayin da aka makale su a samansa.

Dan adaidaita ya yi lodi na manyan tankunan ruwa

Kara karanta wannan

Abun Farin Ciki: Daga Karshe Lauya Ya Gano Ainahin Masu Gidan Da Aka Yasar Tsawon Shekaru 30 a Kaduna, Hotuna Sun Bayyana

A cikin bidiyon, direban ya yi kokarin tuka Keken a unguwanni, amma da kyar ya sha domin ya fuskanci gargada a titi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adaidaitan na ta yin gaba sannan ya yi baya amma ya gaza tafiya daidai saboda lodin ya yi yawa kuma ga hanyar babu kyau.

Mutane da dama sun yi ta kallo cike da mamaki yayin da dan adaidaitan ke kokarin isa masaukinsa.

Shafin Gistlover ne ya wallafa hoton a shafin Twitter.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@nwanyi_ocha ya ce:

"Da wannan tsadar man fetur din na yanzu, ba sa so su dauki kasadar tuki sau biyu."

@UncleOsas_ ya yi martani:

"Dole ya zamana a jihar Dela ne, suna amfani da keke wajen daukar gida ma a wannan wajen."

@SamuelOtigba ya ce:

"Ina ruwan dan gareji da lodi ya yi yawa."

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

@Oyoro4 ya yi martani:

"Wasu masu tukin adaidaita sun zata Mack suka dauko."

@OnyeAdugbo ya ce:

"Wannan rashin hankali ne. Idan ya ji wa kansa ko kekensa rauni, zai ce sharrin shaidan ne."

@olushayhe ta yi martani:

"Don Allah nawa za su biya wannan mai adaidaitan da wannan lodi mai yawa?"

Ciki ya sauyawa kyakkyawar budurwa halitta

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar mata da ke tsammanin za ta kara kyau idan ta samu juna biyu ta sha mamaki sannan ta ga zahiri bayan yanayinta ya sauya, kamar yadda wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna.

Bidiyon ya nuno yanayinta kafin da bayan ta dauki juna biyun, yana mai nuna banbancin da aka samu tun daga kalar fatarta har zuwa yanayin halittarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel