Yadda Juna Biyu Ya Sauya Kyakkyawar Budurwa Ta Zama Wata Daban, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yadda Juna Biyu Ya Sauya Kyakkyawar Budurwa Ta Zama Wata Daban, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wata matashiyar mata da ke sa ran kara kyau yayin da take dauke da juna biyu amma ya zo da akasin haka ya yadu a TikTok
  • Bidiyon ya nuno yadda take da kyau kafin ta dauki cikin da kuma yadda ta sauya gaba daya bayan daukar sa
  • Ta kara baki sannan ta yi zuru-zuru, wanda hakan ke nuna kowace mace da yadda ciki ke yi da ita

Wata matashiyar mata da ke tsammanin za ta kara kyau idan ta samu juna biyu ta sha mamaki sannan ta ga zahiri bayan yanayinta ya sauya, kamar yadda wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna.

Bidiyon ya nuno yanayinta kafin da bayan ta dauki juna biyun, yana mai nuna banbancin da aka samu tun daga kalar fatarta har zuwa yanayin halittarta.

Kara karanta wannan

Yadda Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

Matashiya ta kara muni bayan da ta dauki juna biyu
Matashiya Ta Zata Ciki Zai Kara Mata Kyau Amma Sai Ya Shayar Da Ita Mamaki, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: TikTok/ @x_taclie
Asali: TikTok

Budurwa ta sauya gaba daya bayan ta samu juna biyu

Ta sauya daga wata kyakkyawar mace zuwa baka sannan ta yi zuru-zuru, wanda hakan ke nuna ba kowace mace ce za ta iya fuskantar sauyin da ciki ke zuwa da shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Resa Chi:

"Me yasa juna biyun Najeriya ya banbanta da saura! Ina so na yi kamar Rihanna don Allah faa."

ALI EKOCHE AGATHA:

"Duk kuna sa batun cikin nan kada ya zo kaina ya zama abun tsoro kada na zama wata halitta fa."

Aminudolipartin:

"Ahhhh wannan babban lamari ne fa na tabbata ita/shi zai yi kyau sosai."

Kezia Carroll:

"Wayyo Allah nice wannan a yanzu cikin watanni dauke da kuraje masu yawa bana ma iya gane kaina."

Kara karanta wannan

Malamar Makaranta Ta Sharbawa Daliba Zane 4 a Fuska, Mahaifiyar Yarinyar Ta Saki Hotuna

Rukia:

"Fuskata ta washe sosai lokacin da nake da juna biyu kuma cikina bai nuna ba har sai da na kai makonni 34."

Singathwa:

"Ke ce dai dauke da kwaliyya da wanda babu kwaliyya."

Ugoonma:

"Addu'ata a kullun na kasance tare da wani mutum da ya cancanci wannan sauyin."

Mata mai juna biyu ta koka bayan cikinta ya ki bayyana

A wani labarin, wata mata mai ɗauke da juna biyu mai amfani da sunan @welly.james a TikTok, ta bayar da mamaki bayan ta nuna cikinta ɗan ƙarami wanda bai bayyana ba sannan ta yi iƙirarin cewa juna biyunta ya kai wata biyar.

A cikin bidiyon ta nuna cikinta wanda bai nuna alamun cewa tana ɗauke da jariri a cikinsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel