Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Barazanar Soke Adaidaita Sahu A Yankinsa, Ya Bayyana Dalilai

Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Barazanar Soke Adaidaita Sahu A Yankinsa, Ya Bayyana Dalilai

  • Shugaban karamar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa ya gargadi masu adaidaita sahu kan aikata muggan laifuka a yankin
  • Thomas James ya ce yana dab da hana masu adaidaita sahun a karamar hukumar ganin yadda aikata laifuka ke karuwa
  • Thomas ya rushe shugabannin kungiyar tare da nada kwamiti mai dauke da mutane biyar don shawo kan wannar matsalar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Nasarawa – Shugaban karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, Mista James Thomas ya yi barazanar hana masu adaidaita sahu aiki a yankin.

James ya bayyana haka ne yayin ganawa da kungiyoyin masu adaidaita sahu da masu babura a ranar Alhamis 6 ga watan Yuli a Karu.

Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Barazanar Soke Adaidaita Sahu a Yankinsa
Shugaban Ya Ce Zai Soke Adaidaita Sahun Ne Saboda Dakile Rashin Tsaro. Hoto: Facebook.

Ya ce matakin bai rasa nasaba da yawan aikata laifuka a karamar hukumar dalilin masu adaidaita sahun wanda ke bukatan matakin gaggawa, Pulse ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shafe Harajin da Aka Lafta, Ya Ƙirƙiro Dokokin Rage Raɗaɗi

Ya bayyana cewa matakin soke masu adaidaita sahun an yi ne don inganta tsaro

Yayin da ya ce mafi yawan laifuka da ake aikatawa a karamar hukumar ana fakewa ne da masu adidaita sahun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Ba zamu lamunta ba, mu masu son zaman lafiya ne a Karu don haka babu wani ta’addanci da zamu amince da shi a wannar karamar hukuma.

Shugaban ya ba da misalin jihohi da kuma wasu yankuna a birnin Tarayya da suka hana masu adaidaita sahun, inda ya gargade su da cewa idan aikata muggan laifuka suka ci gaba to lallai ba shi da wani zabi illa soke adaidaita sahun.

Shugaban ya rusa dukkan shugabannin kungiyar tare da nada nashi kwamiti

Ya kara da cewa:

“Dukkan shugabannin kungiyoyin an rusa su saboda sun yi yawa yadda ba za a iya sanin abubuwan da ke gudana ba.

Kara karanta wannan

Masu Adaidaita Sahu Sun Yi Tafiyar Kilomita 757 Daga Wata Jiha Zuwa Abuja Don Karrama Tinubu

“Daga yau na nada kwamiti mai dauke da mambobi biyar da na amince da su tsawon shekaru wadanda za su yi saurin gano masu adaidaita sahun idan an aikata wani laifi.
“Wannan zai taimaka wurin zakulo wadanda suke aikata laifi a kungiyar don hukuntasu dai-dai da laifinsu.

Kwamandan yanki na jami’an ‘yan sanda, ACP Francis Obigwa yayin bayaninsa, ya gargadi masu adaidaita sahun da su guji daukar doka a hannunsu.

Karamar hukumar Karu a baya ta sha alwashin hana masu adaidaita sahu aiki a yankin musamman wadanda ba su da rijista, cewar rahotanni.

Masu Adaidaita Sahu Sun Shafe Kilomita 757 Daga Lagos Zuwa Abuja Don Karrama Tinubu

A wani labarin, kungiyar masu adaidaita sahu reshen Ajah sun niki gari daga jihar Lagos har Abuja don yabawa Shugaba Tinubu.

Shugaban kungiyar a yankin, Babatunde Olisah ya ce sun shafe kilomita 757 musamman don kawo wa Tinubu ziyara.

Kara karanta wannan

Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 Da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

Ya ce mutanen Najeriya sun daura buri sosai a wannan gwamnati inda ya roki shugaban da kada ya watsa musu kasa a ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel