"Majalisun Dokoki na Jihohi 4 ba Su Mika Matsayarsu kan Kafa Yan Sandan Jihohi ba"

"Majalisun Dokoki na Jihohi 4 ba Su Mika Matsayarsu kan Kafa Yan Sandan Jihohi ba"

  • Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce majalisun dokokin jihohi huɗu ba su aika da matsayarsu kan shirin kafa ’yan sandan jihohi ba
  • Ya bayyana cewa hakan ba zai hana Majalisar Tarayya ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulki da miƙa kudirin ga shugaban ƙasa domin amincewa ba
  • Bamidele ya ce tsarin ’yan sandan jihohi ba wai an ƙirƙire shi ne domin kafa rundunonin ’yan sanda na ƙabila ko jiha ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa majalisun dokokin jihohi huɗu daga cikin 36 ba su aika da matsayarsu kan shirin kafa ’yan sandan jihohi ga Majalisar Tarayya ba.

Sanata Bamidele, wanda ke wakiltar mazaɓar Sanatan Ekiti ta Tsakiya, ya ce duk da cewa Majalisar Tarayya na ci gaba da jiran rahotannin jihohin huɗun, rashin aika su ba zai hana ’yan majalisar tarayya ci gaba da aikin ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Opeyemi Bamidele.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Opeyemi Bamidele Hoto: @mob_sen_leader
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani bikin bayar da kyaututtuka da kamfanin The Sun Publishing Limited, mawallafin jaridar The Sun, ya shirya a Abuja.

Yadda Majalisar dattawa ta sa wa'adi

Premium Times ta ruwaito cewa an karrama Bamidele da lambar yabo ta Sanatan Shekara a wannan taron.

A ranar 4 ga watan Nuwamba, yayin zaman majalisa, Majalisar Dattawa ta sanya ranar 15 ga watan Nuwamba, 226 a matsayin wa’adin da majalisun dokokin jihohi za su aika da matsayarsu kan shirin kafa ’yan sandan jihohi.

A lokacin, jihohi shida ba su aika da rahotanninsu ba. Jihohin sun haɗa da Kano, Oyo, Cross River, Abia, Niger da Benue.

Majalisa na jiran matsayar jihohi 4

Sai dai yayin da yake magana kan batun, Bamidele bai bayyana sunayen majalisun dokokin jihohin biyu da suka aika matsayarsu tun bayan sanya wa’adin ba, ko kuma waɗanda har yanzu ba su cika sharadin ba.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

“Yanzu muna jiran majalisun dokokin jihohi huɗu su gabatar da rahotanninsu kafin ko kuma ranar da Majalisar Tarayya za ta koma zama a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2026.
"Wannan na nuna cewa mako mai zuwa zai kasance muhimmin lokaci ga Majalisar Tarayya. Ko sauran jihohin sun aika da rahotanninsu ko ba su aika ba, dole ne mu ci gaba domin cika burin al’ummarmu,” in ji shi.

Matakin Majalisar dattawa na gaba

Bamidele ya ce Majalisar Tarayya za ta miƙa kudirin ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu domin samun amincewarsa, saboda muhimmancin hakan ga zaman lafiya, ci gaba da kwanciyar hankalin ƙasa.

“Yanzu nauyi ne a kanmu mu miƙa Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na 2026 kan ’Yan Sandan Jihohi ga shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin sojojin ƙasar nan, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, GCFR, domin ya amince da shi.
"Wannan nauyi ne da dole ne mu sauke da sanin ya kamata a madadin al’ummomin da muke wakilta, da kuma domin zaman lafiya, ci gaba da kwanciyar hankalin ƙasa,” in ji shi.
Majalisa.
Sanatoci yayin da suke tsakiyar zama a zauren Majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Jawaban Bamidele sun nuna cewa kudirin ya samu amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi 36, wanda ya yi daidai da jihohi 24.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce ya gano tarkon da Tinubu ya kafa masa kan bashin da zai ci a waje

Fadar shugaban kasa ta yi bayani

Kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen shirin kafa ‘yan sandan jihohi da nufin inganta tsaro a Najeriya.

Ta ce yanzu an samu fahimtar juna a fadin kasa kan bukatar kafa ‘yan sandan jihohi, inda tattaunawa ta wuce matakin ko za a yi tsarin zuwa yadda za a aiwatar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262