Tsadar Mai: An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Direbobin Tasi da Adaidaita Sahu, Direba Ya Bayyana Dalilin Fadan

Tsadar Mai: An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Direbobin Tasi da Adaidaita Sahu, Direba Ya Bayyana Dalilin Fadan

  • Wasu direbobin tasi da na adaidaita sahu sun bai wa hamata iska akan farshin daukar fasinja a jihar Ondo
  • Direbobin tasi din sun zargi masu adaidaita sahu da daukar fasinja a kudi mai rahusa sabanin yadda ake kara
  • Bayan cire tallafin man fetur, an samu matsaloli da dama ciki har da karin farashin litar mai a fadin kasar

Jihar Ondo – Mutane da dama sun shiga wani yanayi a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu, saboda tsadan man fetur a fadin kasar.

An samu hatsaniya tsakanin masu adaidaita sahu da masu tasi saboda farashin sufuri bayan tashin farashin man fetur.

An yi rikici tsakanin masu adaidaita sahu da yan tasi
An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Direbobin Tasi da Adaidaita Sahu. Hoto: Wealth Result
Asali: Facebook

Direbobin tasi din sun zargi masu adaidaita sahu da daukar fasinja a kudi mai rahusa sabanin yadda su suke dauka saboda karin farashin man din.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Menene dalilin fadan a tsakaninsu ?

Tribune ta tattaro cewa direbobin tasi sun kara kudin motar tafiya daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUTA) zuwa kasuwar Ojaoba daga N200 zuwa N300, amma masu adaidaita sahu suna daukar fasinja a N200 kacal.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Direbobin tasi din sun tara dukkan ‘yan uwansu don hana masu adaidaita sahun daukar fasinja a wannan farashi, cewar Vanguard.

Mafi yawan fasinjojin sun koma hawa babur na ‘yan acaba don samun sauki yayin da ake ta rikici tsakanin direbobin tasi da adaidaita sahu, akan karin farashin.

Wani direba ya ce sulhu suke so su yi a tsakaninsu

Wani direba mai suna Mista Olawale Ajayi ya ce ba fada suke da masu adaidaita sahu ba kawai suna bukatar amincewarsu ne akan karin farashin kudin.

A cewarsa:

“Mun taru anan ne saboda fasinjoji sun ki yarda su biya sabon farashi N300, amma masu adaidaita sahu suna daukar fasinja akan N200 maimakon N300.

Kara karanta wannan

An Tura Maniyyata Zuwa Aikin Hajji a Saudi Su Kadai Saboda Rashin Biyan Kudi

“Ba zamu samu kudi ba idan muka ci gaba da daukarsu a tsohon farashi, yadda masu adaidaita sahu suke dauka yana cutar damu, muna so mu tattauna da su.”

Wani direba ya kara da cewa, ba za su iya kai balas na N4,000 ba idan suka sayi lita 30 akan kudi N15,000.

NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

A wani labarin, Kamfanin man fetur, NNPC ya kara farshin man fetur a gidajen mai da ke karkashinsa.

Kakakin kamfanin, Garba Deen Muhammad ne ya bayyana haka inda ya ce farashin ya yi daidai da yadda kasuwa ya ke a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel