Shugaba Tinubu Ya Musanta Batun Karin Kudin Haraji a Ƙasar Nan

Shugaba Tinubu Ya Musanta Batun Karin Kudin Haraji a Ƙasar Nan

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi fatali da rahotannin cewa gwamnatinsa na shirin ƙara harajin da ƴan Najeriya ke biyan gwamnatin tarayya
  • Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin garambawul kan harkokin haraji, shi ne ya musanta rahotannin a ranar Talata
  • A cewar Oyedele, abin da gwamnati ke shirin yi shi ne rage sama da haraji 60 da ake biya ga hukumomi daban-daban zuwa waje ɗaya

FCT, Abuja - An yi fatali da rahotannin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu yana shirin ƙara yawan harajin da ƴan Najeriya su ke biyan gwamnatin tarayya.

Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin tsare-tsare da garambawul kan harkokin haraji, a martanin da ya yi kan rahotannin ranar Talata, ya bayyana cewa gwamnati ba ta da shirin ƙara wani haraji, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja

Tinubu musanta batun kara kudin haraji
Shugaba Tinubu ya musanta shirin kara kudin haraji Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

A cewar masanin a harkokokin harajin gwamnatin Tinubu na duba yiwuwar rage sama da haraji 60 da ake biya zuwa waje ɗaya.

Oyedele ya ƙara nuni da cewa maƙasudin yin hakan shi ne tattara harajin wajen ɗaya ta yadda babu buƙatar biyan sama da haraji 10 a matakan gwamnatoci daban-daban, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu na son mayar da haraji waje ɗaya

A kalamansa:

"Muna da ƙwarin gwiwar cewa hakan abu ne mai yiwuwa idan aka ba mu goyon baya. Za mu ci gaba da yin abin da za mu iya domin rage haraji kan kuɗaɗen shiga a maimakon ƙara haraji."
"Za mu gudanar da zaman mu na farko a sati mai zuwa, inda za mu sanar da ƙarin bayanai daga nan."

Shugaba Tinubu a ranar Talata, 8 ga watan Agusta ya kaɗɗamar da kwamitin na yin garambawul kan harkokin haraji, wanda daga cikin mambobin kwamitin akwai Orire Agbaje wata ɗalibar ajin ƙarshe a jami'ar Ibadan (UI).

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Shugaban ƙasar ya ƙaɗdamar da kwamitin ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

Ba Shirin Dawo Da Tallafin Mai, FG

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya musanta batun sake dawo da tallafin man fetur.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa an wuce da batun tallafin man fetur, sanann babu buƙatar yin kwan gaba kwan baya kan batun tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng