Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin da Zai Gyara Harkar Tattalin Arziki da Haraji

Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin da Zai Gyara Harkar Tattalin Arziki da Haraji

  • Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da kwamitin da za su yi aikin farfado da tattalin arzikin Najeriya
  • An ba kwamitin alhakin yi wa tsare-tsaren haraji garambawul sannan a kawo hanyoyin cigaba
  • Taiwo Oyedele wanda ya yi aiki da kamfanin PriceWaterhouseCoopers ne zai jagoranci aikin

FCT, Abuja – Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamiti na musamman da zai kawo gyare-gyaren manufofin tattalin arziki a Najeriya.

Tashar yada labarai ta Channels ta ce an yi bikin kaddamar da kwamitin shugaban kasar ne a fadar Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Mai taimakawa Shugaban Najeriya wajen harkoki na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ya fitar da wata sanarwa ranar Talata.

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu tare da Orire Agbaje Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Gwamnatin Tinubu ta jawo Oyedele

Kwamitin zai zama karkashin jagorancin kwararren masani a harkar haraji da kudi kuma shugaba a PriceWaterhouseCoopers, Taiwo Oyedele.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taiwo Oyedele da sauran ‘yan kwamitin da aka zakulo dagaciki da wajen gwamnati za su taimaka wajen kawo dokoki da duk tsare-tsaren tattali.

Jaridar Punch ta ce kwamitin zai fito da hanyoyi tare da tsara yadda za a rika tattara haraji a Najeriya ba tare da an rika samun tufka da warwara ba.

Dabarun da Tinubu ya fara da su a ofis

Da yake bayani dazu, Bola Ahmed Tinubu ya ce tun da ya shiga ofis, yake kokarin ganin an canza fasali tare da farfado da tattali arzikin kasar nan.

Kafin a tafi ko ina, Mai girma shugaban Najeriya ya tunawa kwamitin yadda ya cire tallafin fetur, daga nan kuma ya soke yadda aka saba saida kudin waje.

"Duk da mu na bukatar muhimman matakan nan biyu, mun san gyare-gyaren da za mu yi ya na da zurfi, idan mu na so mu daidaita kasarmu, mu kawo cigaba.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

Jama’a sun sa tsammani a kan gwamnatinmu, su na sa ran mu inganta rayuwarsu. Ba za mu zarge su da daura mana tunanin da da ya fi karfinmu ba.
Duk wanda ya saye rariya, ya san za ta zubar da ruwa, musamman da mu ka dauki alkawari.
Na sha alwashin amfani da duk wata sa’a da zan yi a ofis wajen inganta rayuwar mutanenmu."

- Bola Tinubu

Kun san labarin Orire Agbaje?

Tinubu ya ce ana bukatar haraji idan aka duba karfin tattalin arziki da bashin da ake bin Najeriya.

Hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada ya ce a 'yan kwamitin har da wata dalibar tattalin arziki, Orire Agbaje da ke ajin karshe a jami'ar Ibadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel