Hukumar Kwastam Ta Jihar Ogun Ta Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye a Cikin Buhunan Shinkafa

Hukumar Kwastam Ta Jihar Ogun Ta Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye a Cikin Buhunan Shinkafa

  • Hukumar kwastam ta jihar Ogun, ta sanar da kama harsasan bindiga 1,245 da aka shigo da su daga waje
  • Hukumar ta ce an ɓoye harsasan ne a cikin buhunan shinkafa yar ƙasar waje guda 20 da aka shigo da su
  • Hukumar ta samu muhimman bayanai na sirri, wanda da su ne ta yi amfani wajen cafke kayan laifin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, jihar Ogun - Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa (NCS), reshen jihar Ogun, ta ce jami'anta sun kama harsasan bindiga 1,245 da aka boye a cikin buhunan shinkafa 'yar ƙasar waje.

Kwamandan rundunar kwastam na yankin, Bamidele Makinde ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Abeokuta ranar Litinin.

Hukumar kwastam ta yi nasarar cafke harsasan bindiga da aka shigo da su
Hukumar kwastam ta kama harsasan bindiga 1,245 a jihar Ogun. Hoto: Leadership News, PM News
Asali: UGC

Yadda jami'an kwastam suka kama harsasai 1,245 a jihar Ogun

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Hukumar NBTE Ta Kaddamar Da Shirin Karatun Mayar Da Kwalin HND Zuwa Na Digiri Cikin Shekara 1

Bamidele ya ce hukumar kwastam ta jihar ta samu bayanai na sirri cewa wasu na ƙoƙarin shigowa da muggan makamai daga ƙasar Benin kamar yadda PM News ta wallafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa duba da irin ɓarnar da za a yi da makaman idan aka yi nasarar shigowa da su ne ya sanya jami'an hukumar zage damtse wajen sanya idanu kan iyakar Najeriya da Benin da ke jihar Ogun.

Ya ƙara da cewa jami'ansu waɗanda ke aiki dare da rana, sun yi nasarar kama motoci biyar ƙirar Toyota ɗauke da buhuna 203 na shinkafa 'yar ƙasar waje.

Yadda aka gano harsasan da ke cikin buhunan shinkafar

Bamidele ya kuma ce direbobin motocin sun fice daga motocin, sannan suka ranta a na kare zuwa cikin daji a lokacin da suka lura da jami'an na neman kama su.

Kara karanta wannan

Firaministan Nijar Ya Fadi Abinda Za Su Yi Dangane Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mu Su

Bayan kama kayayyakin ne jami'an suka bincikesu kaf, inda suka samu harsasan bindigar guda 1,245 a cikin buhuna 20 na shinkafa.

Jaridar Leadership ta bayyana cewa jamhuriyar Nijar ake shirin kai harsasan bindigar da aka kama a kan iyakar ta Ogun.

Hukumar Kwastam ta yi bayani kan dalilin rufe iyakokin Najeriya da Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan dalilin rufe iyakoki tsakanin Najeriya da jamhuriyar Nijar da hukumar kwastam ta bayar.

Hukumar ta kwastam ta bayyana cewa hakan ba wai yana nufin ƙulla yaƙi tsakanin ƙasashen guda biyu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel