Tsadar Fetur: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Haske a Kan Sake Maido Tallafin Mai

Tsadar Fetur: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Haske a Kan Sake Maido Tallafin Mai

  • Maganar cewa gwamnatin tarayya za ta sake fito da tsarin biyan tallafin man fetur ba gaskiya ba ne
  • Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa an yi sallama da tsarin, babu niyyar a rika yin gaba da baya
  • Mai ba shugaban Najeriya shawara, Tope Ajayi ya tabbatar da wannan da ya ke bayani a shafin X

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Babu wani shirin da ake yi na sake maido tallafin man fetur watanni kusan uku kenan bayan an bada sanarwar janye tsarin a Najeriya.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya musanya rahotannin da aka fitar a farkon makon nan, ya jaddada yin ban-kwana da biyan tallafin man fetur.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin Tope Ajayi a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter, ya ce gwanatinsu ba ta da niyyar lashe aman da ta yi.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Tsadar Fetur: Fadar Shugaban Kasa
Fetur ya yi tsada a mulkin Bola Tinubu Hoto: TheTope_Ajayi
Asali: Twitter

Tope Ajayi ya karyata maganar cewa tallafin fetur zai dawo na tsawon wucin gadi a sakamakon yadda litar fetur ke neman tashi zuwa fiye da N700.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Babu shirin maido kowane nau’i na tallafin man fetur. Babu yanayin da za ayi daukar dawainiyar wani karin farashi a wannan lokaci.
Shugaba Tinubu ya gamsu da bayanan da yake da shi cewa za a iya cigaba da aiki da farashin ba tare da dawo da hannu agogo baya ba."

- Tope Ajayi

Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen yada labarai ya bayyana cire tallafin a matsayin wata hanyar gyara kwamacalar cikin harkar fetur.

Bayan cire tallafin, karyewar Naira da tashin Dalar Amurka ya taimaka wajen tsadar man. NLC ta na barazanar tafi yajin-aiki idan kudi ya karu.

Har gobe fetur akwai araha a Najeriya

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

The Nation ta ce Tinubu ya ce an kama hanyar ganin farashin fetur ya tsaya a yadda ya ke, sannan ba tare da ya biya sisin kobo da sunan tallafi ba.

Gwamnatin tarayya ta na ikirarin ta cire hannunta daga harkar, ta bar farashi ya rika juyawa duk yadda kasuwa ta buga, hakan ya jawo matsin lamba.

Fadar shugaban kasa ta ce duk da haka a Sanagal, Guinea, Cote d’Ivoire, Mali da CAR, ana saida litar fetur ne a kan N1273, N1075, N1048, N1113 da N1414.

Buhun shinkafa zai kara tsada

Rahoto ya zo mana cewa masu casar shinkafa a wasu yankunan Arewa su na kukan cewa babu kayan gona da za su sarrafa, kaya sun kare a kasuwa.

Maganar da ake yi, an rufe wasu iyakokin Najeriya, dala ta tashi kuma ba a samu isasshen kayan gona saboda rashin tsaro da rashin ruwan sama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel