Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

  • Diyar biloniya Muhammed Indimi, Meram ta shiga daga ciki a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta
  • Hotunan bikin Meram da hadadden angonta kuma dan kasuwar kasar Turkiyya ya yadu a shafukan soshiyal midiya
  • Mutane da dama sun taya ma'auratan murna, inda wasu suka ce sun matukar dacewa da juna domin dai kyau ya hadu da Kyau

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Meram Indimi, diyar babban attajirin dan kasuwar Najeriya, Alhaji Muhammed Indimi, ta amarce da hadadden angonta wanda ya kasance dan kasuwar kasar Turkiyya, Yakup Gundogdu.

Yan uwa da abokan amarya ciki har da mahaifiya da yan uwanta mata sun gazaya shafin Instagram don wallafa wasu hotuna daga shagalin bikin.

Diyar Indimi ta shiga daga ciki
Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya Hoto: samira_sheriff
Asali: UGC

An dai daura auren tare da liyafar bikin ne a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: An yi auren babban dan El-Rufai amma bai halarta ba, bayanai sun fito

Da take wallafa hotunan biki, mahaifiyar amaryar, Samira Sheriff ta rubuta a Instagram:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An yi an gama gimbiyata @princess.m.i, kalamai ba za su iya bayyana irin murnar da nake maki ba a wannan sabuwar rayuwa ta ki. Allah ya albakaci aurenki, Allah ya sa ya cika da kauna, farin ciki da yarda. Ina matukar farin ciki kin samu irin namijin da kike mafarki, soyayya ta gaskiya, kuma na samu sabon 'da @yakupgundogduu0 .”

Meram ta taba auren wani dan siyasa mai suna Baffa Dandatti Abdulkadir a 2018 kafin suka rabu daga baya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jama'a sun taya sabbin ma'auratan murna

sheefarh' ta yi martani:

"Allah ya sanya alheri."

hausilambara ta ce:

"Kyakkyawan hadi."

mashaschops_ ta ce:

"Ina taya ki murna @princess.m.i Allah ya albarkaci gidanki Ameen ya rabbi."

Kara karanta wannan

An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali

mummyzainab ta ce:

"Alhamdullah. Allah ya albarkaci aurenki ta kowani hanya ❤️"

halliesabdul ta ce

"Allahummah Barik! Allah ya albarkaci aurensu."

hassieshine ta ce:

"Ameen ya rabb! ina taya ki murna Meram! abun ya yi kyau sosai! ❤️"

algoniarab ya ce:

"Ina taya yar kanwata murna ❤️."

Hotuna daga shagalin bikin dan El-Rufai

A wani labarin, mun ji cewa an sha shagalin bikin Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna ta arewa a majalisar wakilai.

A watan Mayun shekarar nan ne aka daura auren Bello da amaryarsa Aisha Shuaibu a wani biki da aka yi cikin sirri a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel