Ayar Tambaya Yayin da Aka Yi Auren Babban Dan El-Rufai, Amma Bai Halarci Bikin Ba

Ayar Tambaya Yayin da Aka Yi Auren Babban Dan El-Rufai, Amma Bai Halarci Bikin Ba

  • Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya auri matar ta biyu mai suna Aisha Habibu Shuaibu
  • Mahaifinsa, Nasir El-Rufai, abin da ya bayyana a fili dai bai halarci daurin auren dan majalisar wakilan ba
  • Idan dai za ku iya tunawa, an ruwaito cewa El-Rufai ya fice daga kasar ne bayan yin sallama da aniyar zama minista

Kaduna, Jihar Kaduna – Abin da ya bayyana a fili ya nuna cewa, Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, bai halarci wurin daurin auren babban dansa ba, Bello.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Bello El-Rufai ya auri matar ta biyu mai suna Aisha Habibu Shuaibu a ranar Asabar 13 ga watan Agusta.

Ku tuna cewa tsohon gwamnan ya fita daga Najeriya ne a lokacin da yake jiran amincewar majalisar dattawa domin tantance shi a matsayin ministan Tinubu.

Kara karanta wannan

An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali

An yi auren dan El-Rufai ba ya nan
Lokacin da ake biki | Hoto: @B_ELRUFAI
Asali: Twitter

Yadda aka ki amincewa da batun ministan El-Rufai

A makon da ya gabata ne majalisar ta tabbatar da nadin ministoci 45 daga cikin 48 da shugaba Bola Tinubu ya mika mata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, akwai mutane uku da majalisar ta dakatar da batun tantance su, daga ciki har da El-Rufai, Stella Okotete daga Delta da Danladi Abubakar daga jihar Taraba.

A ranar Talata, 8 ga watan Agusta, rahotanni sun ce tsohon gwamnan ya gana da shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja kafin ya tafi kasar waje, rahoton Leadership.

Ina El-Rufai ya fece ya tafi?

Majiyoyin fadar shugaban kasar sun bayyana cewa jigon na jam'iyyar APC zai kasance a nahiyar Turai amma zai fara sauka a kasar Masar da fari.

An dai yi ta cece-kuce kan gazawar majalisar dattawa wajen tabbatar da nadin El-Rufai a matsayin ministan Tinubu.

Kara karanta wannan

Kujerar Minista: Uba Sani Ya Magantu Kan Zargin Yi Wa El-Rufai Tuggu a Wurin Tinubu

A bangare guda, dansa Bello ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan dokokin banki. Ya yi aure na biyu ne da diyar tsohon shugaban mulkin soja na jihar Filato da Neja, Habibu Shuaibu, a Abuja.

Yaya batun maye gurbin El-Rufai?

A bangare guda, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya musanta wani labari da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke cewa shi ya ki amincewa da sunan Nasir El-Rufai a matsayin minista daga jihar.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya zabi El-Rufai a matsayin minista amma har yanzu majalisar dattawa ba ta amince ba, inda ta ce akwai wasu korafe-korafen tsaro da ake yadawa a kan tsohon gwamnan na Kaduna.

An ce El-Rufai ya gana da Tinubu ya ce masa ba ya sha’awar zama minista a yanzu, kuma Jafaru Sani tsohon kwamishinansa ya shawarta a dauka a maye gurbinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel