Diyar Biloniya Hauwa Indimi Ta Koka Kan Siyan Tumatir N8k

Diyar Biloniya Hauwa Indimi Ta Koka Kan Siyan Tumatir N8k

  • Diyar biloniya Mohammed Indimi, Hauwa, ta garzaya soshiyal midiya don kokawa a kan tsadar rayuwa a kasar
  • Matashiyar ta koka bayan ta siya karamin kwandon tumatir kan N800 sannan ta saki hoton a soshiyal midiya
  • Wallafar Hauwa Indimi ya haddasa cece-kuce daga yan Najeriya bayan ya yadu a shafukan zumunta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hauwa Indimi Yar’adua, diyar biloniya Mohammed Indimi, ta koka kan hauhawan farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar nan.

Duk da kasancewarta diyar biloniya, alamu sun nuna Hauwa ta fara jin radadin tsadar da kayan abinci suka yi a kasuwa.

Hauwa Indimi ta koka kan tsadar tumatir
Diyar Biloniya Hauwa Indimi Ta Koka Kan Siyan Tumatir N8k Hoto: @hauwaindimi
Asali: Instagram

Hauwa ta wallafa hoton wani dan karamin kwandon tumatir da ta siya a kan farashi mai yawa. A cewarta, har yanzu abun ya kasa barin zuciyarta.

Ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

"Na tura mutanena kasuwa a jiya, wannan tumatir din N8k ne. Har yanzu abun ya kasa barin raina."

Ga hoton wallafar da ta yi a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani a kan wallafar Hauwa Indimi

l.tobiloba:

"Abun takaici ne cewa dole duk sai mun azabtu sakamakon rashin hankalin wadanda suka zabi uban yan haraji. Nan ba da dadewa za ku fara biyan kudin iskar da kuke sha, yanzu aka fara shan wuya."

Savvyrinu:

"Ba sai kun ci tumatir ba. Ku yi amfani da karas. a kan zabenku."

d_sozogold:

"Sannan mu manoma da muke son samar da wadannan abubuwa domin su wadatu bamu da ikon yin noma cikin kwanciyar hankali. Garkuwa da mutane da kashe-kashe a gona. Tsadar noma ya hauhawa. Akwai mafita ga wannan annobar amma babu goyon bayan da zai sa yayi aiki. Ina mafita don Allah."

Baby_gender1:

"Ka yi tunani wani hali masu karamin karfi ke ciki."

Kara karanta wannan

Muje Zuwa: El-Rufai Ya Magantu Kan Yadda Kamun Ludayin Gwamnatin Shugaba Tinubu Ya Kawo Sauyi

evelyn____xx:

"Idan masu kudi na korafi toh ka duba yaya talaka zai yi kenan."

thefoodnetworknig2:

"Idan diyar biloniya za ta iya korafi, hakan na mufin kawai su ba talakawa irinmu igiya...kawai ku shake mu."

debbie_gowal:

"Ka yi tunanin ya mai rufin asiri a Najeriya ke ji game da tsadar rayuwa a kasar nan..."

legit.ng ta zanta da Mallam Mansir mai kayan gwari a kasuwar gwadabe da ke garin Minna, inda ya ce ba laifinsu bane tsadar da kayan miya suka yi.

Mallam Mansir ya ce:

“Ba laifinmu bane, misali kin ga ko mu wannan tsadar kayan ya shafe mu saboda mutane basa siya yanzu, masu siyan tumatir sun ragu ba kadan ba. Daga chan inda muke siyo kayan abun ba’a magana sannan a zo maganar kudin motar daukar kaya, wani idan ka yi lissafi wasu kayan kusan babu riba ake siyar da su.
“Tun kafin babban sallah muke ta sa ran tsadar abubuwa za su ragu sabona muna ta tsimayin tumatir yan Kamaru da sauransu za su shigo, amma sai abun ya kasance akasin haka. Kawai sai dai ayi addu’a Allah ya kawo mana dauki.”

Kara karanta wannan

TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

Matashi ya tsere bayan shafe watanni hudu a otel din alfarma, mai biya ko sisi ba

A wani labari na daban, yan sanda na neman wani mutum mai suna Mohammed Sharif.

Sharif ya yi sojan gona a matsayin ma’aikacin gidan sarautar Abu Dhabi sannan ya shafe watanni hudu a wani otel din alfarma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel