Zunubai 10 Da DSS Suka yi Amfani Da Shi a Kan El-Rufai Wajen Tantance Ministoci

Zunubai 10 Da DSS Suka yi Amfani Da Shi a Kan El-Rufai Wajen Tantance Ministoci

  • Wasu abubuwa da-dama su ka hana Nasir El-Rufai a amincewa Nasir El-Rufai ya zama Minista
  • Ana zargin DSS ta fake da irin kalamai da ayyukan ‘dan siyasar wanda za su iya raba kan jama’a
  • Sannan ana tuhumar gwamnatin El-Rufai da jefa al’umma a kangi a sanadiyyar tsare-tsarensa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Zargi dabam-dabam da su ka hada da sakin baki da tulin korafi su ka kawowa Malam Nasir El-Rufai tasgaro wajen zama ministan tarayya.

A rahoton Premium Times, an tattaro jerin zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan, hakan ya jawo aka gaza amince masa da ya rike mukami a gwamnati.

Daga zargin korafi zuwa tauye akkin jama’a, majiya daga hukumar tsaro ta DSS ta bayyana zargin da ake yi wa El-Rufai, sai dai ba mu tabbatar da su ba.

Kara karanta wannan

Kujerar Minista: Uba Sani Ya Magantu Kan Zargin Yi Wa El-Rufai Tuggu a Wurin Tinubu

El-Rufai
Tsohon Ministan Abuja, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

1. El-Rufai bai tsoron sakin maganganu

Rahoton ya ce daga cikin manyan zargin da ake yi wa Malam El-Rufai shi ne ya na yin maganganun da ke iya jawo rikici tsakanin al’ummar Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bayan nan, an ji shi ya na fadawa malaman addini dalilin da ya sa jam’iyyarsa ta APC ta ke tsaida musulmi da musulmi takarar Gwamna a Kaduna.

2. Cin zarafin Bil Adama

Daga zargin da ake yi masa akwai cin zarafi da hakkin al’umma, daga ciki akwai zarginsa da hannu wajen hallaka Ibraheem El-Zakzaky da mabiyansa.

Rikicin Gwamnatin Kaduna da El-Zakzaky ya kai gaban kotun ICC da majalisar dinkin Duniya.

3. Zargin facaka da dukiyar al’umma

A wasu karar da ke gaban kotu da teburin DSS, ana zargin gwamnatin El-Rufai da saida kadarorin gwamnati ga mutanensa da wawurar dukiyar al’umma.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi

4. Jerin korafe-korafe

Tun a majalisa, aka fahimci wasu su na da korafi a kan tsohon ministan, har da wadanda aka aikawa fadar shugaban kasa, majalisar Kaduna da hukumomi.

Sauran zargin da ke wuyan El-Rufai

Rahoton ya ce ba za a rasa kuci-kucin dalilai ba daga cin mutuncin dattawan Arewa, neman soke kotunan shari’a da kuma cin amanar iyayen gidansa a siyasa.

5. Rusa kasuwanni da gidaje da kawo manufofin da za su wahalar da al’umma.

6. Cin amanar iyayen gidansa a siyasa.

7. Zargin ya bayyana Bola Tinubu da mara gaskiya.

8. Kararrarki da su ke kotu a gida da kasar waje

9. Amfani da karfi wajen murkushe abokan adawar siyasa

10. Kisan kare-dangi ga mazauna Kaduna da ganin bayan masu zanga-zanga

Halin da Nasir El-Rufai ya shiga

Nasir El-Rufai bai taba nuna ya na kwadayin Bola Tinubu ya ba shi mukami, amma daga baya ya amince zai yi aiki da gwamnati mai-ci.

A wani lamari mai kama da tuggun siyasa, ana neman hana Malam El-Rufai sake zama Minista, an samu labarin abin da ya kai ya kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel