Dakarun Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno

Dakarun Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar tura ƴam ta'addan ƙungiyar ISWAP masu yawa zuwa inda ba a dawowa
  • Dakarun sojojin a wani luguden wuta da suka yi wa ƴan ta'addan ta sama sun sheƙe ƴan ta'adda 12 har lahira
  • Harin na dakarun sojojin kuma ya lalata kasuwar ƴan ta'addan da raunata da yawa daga cikin mayaƙansu

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun lalata wata haramtacciyar kasuwar ƴan ta'addan ƙungiyar Islamic State of the West African Province (ISWAP) da halaka mayaƙan ƙungiyar masu yawa a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Hare-haren da aka kai ta jiragen yaƙi an kai su ne a ranar 11 ga watan Agusta a Arra, bayan binciken da aka gudanar ya tabbatar da akwai ƴan ta'adda a wuraren.

Sojoji sun halaka mayakan ISWAP
Dakarun sojojin su yi wa mayakan luguden wuta Hoto: Zagazola
Asali: Twitter

Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya samo daga majiya mai tushe cewa an sheƙe ƴan ta'adda 12, an raunata wasu guda shida sannan aka lalata tantunan da su ke amfani da su a matsayin kasuwa.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Iya Tsige Shugaba Tinubu

Wasu ƴan ta'adda sun miƙa wuya

Zagazola ya rahoto cewa jim kaɗan bayan kai hare-haren, ƴan ta'adda takwas suka miƙa wuya a hannun dakarun sojoji na bataliya ta 21 a Bama na atisayen Operation Hadin Kai sannan suka tuba da aikata ta'addanci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan ta'addan da ke laɓewa a yankin, sun addabi manoman da ke a Kawuri, Konduga Bama, wanda hakan ya sanya yakamata a shafe labarinsu gaba ɗaya.

Dakarun sojoji na ƙara matsa kaimi wajen kai hare-hare ta sama da ƙasa kan ƴan ta'addan waɗanda suka daɗe suna aikata ayyukan ta'addanci a jihar ta Borno.

Rikicin ta'addancin na jihar Borno ya salwantar da rayukan mutane masu yawa da asarar dukiyar maƙudan kuɗaɗe, yayin da mutane da dama suka rasa matsugunansu suka koma ƴan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Sun Bayyana Ranar Dawowa Bakin Aiki

'Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5 a Borno

A wani labarin kuma, ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani mummunan hari a jihar inda suka halaka mutum biyar.

Miyagun ƴan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu mata guda bakwai a harin da suka kai kan motocin fasinja da na ɗaukar kaya a ƙaramar hukumar Bama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel