Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Za Su Dawo Aiki Ranar Asabar

Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Za Su Dawo Aiki Ranar Asabar

  • An buƙaci likitoci masu neman ƙwarewa da su koma bakin aikinsu daga ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, a faɗin ƙasar nan
  • Wannan umarnin ya fito ne daga baƙin shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD), Innocent Orji
  • A cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa da ya fitar a daren ranar Juma'a, Orji ya sanar da dakatar da yajin aikin da ƙungiyar ke yi

FCT, Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da dakatar da yajin aikin da take yi a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Innocent Orji, shi ne ya sanar da hakan a daren ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta.

Likitoci sun janye yajin aiki
Likitocin sun hakura da yajin aikin da su ke yi Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Kamar yadda Channels tv ta rahoto, ya bayyana cewa:

"Barka da yamma. Mun dakatar da yajin aiki. Za mu dawo bakin aiki gobe (Asabar) da misalin ƙarfe 8:00 na safe. Za mu yi duba kan ci gaban da aka samu a cikin sati biyu."

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Aike Da Zazzafan Gargadi Zuwa Ga Kasar Rasha

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan matakin na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Buƙatun NARD a wajen gwamnatin tarayya

A cewar shugaban ƙungiyar, likitocin suna neman a biya musu buƙatu takwas ciki har da, ɗaukar sabbin likitoci domin maye gurbin waɗanda suka bar ƙasar nan ko suka rasu.

A kalamansa:

"Mambobin mu suna shan wahala. Ƴan Najeriya na shan wahala. Idan babu likitoci masu yawa a asibiti, hakan barazana ce ga samar da ingantaccen kiwon lafiya. Kuma babu wanda ya fito ya gaya mana cewa abin da mu ke faɗa ba gaskiya ba ne."
"Gwamnati a karan kanta ta kafa kwamiti wanda ya zo da hanyoyin da za a bi tun watan Fabrairun wannan shekarar, meyasa har yanzu ba sanar da su ba?"

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Kungiyar CAN Ta Faɗawa Tinubu Ainihin Matakin Da Ya Kamata Ya Ɗauka

Ya zargi gwamnati da kasa biya musu buƙatun su. Shugabannin Ƙungiyar dai sun gana da wasu sanatoci a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

NARD ta sanar da tsunduma yajin aiki ne a ranar 25 ga watan Yulin 2023, kan buƙatu masu yawa da suka haɗa da ƙarin albashin likitoci.

Sabon Binciken Masana Lafiya

A wani labarin kuma, wani sabon binciken masana a ɓangaren kiwon lafiya ya bayyana adadin takun da mutum yakamata ya riƙa yi a rana domin ƙara tsawancin kwana.

Binciken na masana ya nuna cewa idan ɗan Adam na yin taku 4,000 a rana, hakan zai rage saurin mutuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel