Oluremi Tinubu, Nana Shettima Sun Ziyarci Buhari a Daura

Oluremi Tinubu, Nana Shettima Sun Ziyarci Buhari a Daura

  • Uwargidan shugaban ƙasa ta isa Daura jihar Katsina a ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta domin ziyartar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Sanata Oluremi Tinubu wacce ta samu rakiyar uwargidan mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima, tace ziyarar ta kai ta ne domin nuna godiya ga Buhari bisa halin dattaku da yake nunawa
  • Tsohon shugaban ƙasar ya nuna godiyarsa da jindaɗinsa kan ziyarar da suka kawo masa, inda ya yi nuni da cewa ziyarar abun a yaba ce

Daura, Jihar Katsina - Uwargidan shugaban ƙasa Bola Tinubu, Oluremi Tinubu da uwargidan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, Nana Kashim, sun ziyarci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa dake Daura a jihar Katsina.

Oluremi da Nana sun ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Agustan 2023, cewar rahoton NTA News.

Kara karanta wannan

"Ko Aikin Shara Ne a Aso Villa" Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Roƙi Shugaba Tinubu Alfarma 1 Tak

Oluremi Tinubu ta ziyarci Buhari a Daura
Oluremi Tinubu da Nana Shettima sun ziyarci Buhari a gidansa dake Daura Hoto: @isabature
Asali: Twitter

A wani bidiyo da tashar talabijin ta ƙasa (NTA) ta sanya a shafinta na Twitter, an nuna lokacin da tsohon shugaban ƙasar, ya fito ya tarbi manyan baƙin na sa bayan sun iso cikin gidansa.

Tsohon shugaban ƙasar ya tarbe su cikin raha da barkwanci kamar yadda ya saba tarbar duk manyan baƙinsa. Bayan sun kammala gaisawa da sauran ƴan tawagarsu, Buhari ya yi musu iso zuwa cikin gidan domin tatttaunawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari ya yi magana kan ziyarar Oluremi Tinubu

Tsohon shugaba Buhari a jawabinsa bayan ziyarar, ya nuna godiyarsa inda ya ce ziyarar wacce suka kawo domin ganin yadda yake rayuwa bayan barin madafun iko, abun a yaba ce, rahoton Channels tv ya tabbatar.

A kalamansa:

"Kamar yadda ku ke gani, ta zo ne domin ta duba ni, ta tabbatar cewa ina rayuwa cikin walwala."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Da Sauran Shugabannin APC Sun Shiga Taron NEC, Bayanai Sun Bayyana

Sauran waɗanda suka raka uwargidan shugaban ƙasar wajen ziyarar sun haɗa da, uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Dikko Radda da uwargidan kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hajiya Nasir Daura da sauran jiga-jigan mata na jam'iyyar APC a jihar.

An Bankado Laifin Da Ministan Tinubu Ya Yi Wa Buhari a Baya

A wani labarin kuma, ɗaya daga cikin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa, ya taɓa yin kalamai masu kaushi akan tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buharii.

Bosun Tijani a baya ya sha sukar salon mulki da kamun ludayin gwamnati tsohon Shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel