"Mun Shirya Zama Masu Shara a Villa" Miyetti Allah Ta Roki Tinubu Muƙamai

"Mun Shirya Zama Masu Shara a Villa" Miyetti Allah Ta Roki Tinubu Muƙamai

  • Ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) ta roƙi shugaban ƙasa Tinubu ya waigo kan 'ya'yanta ya naɗa su muƙamai
  • Shugaban MACBAN na shiryyar Kudu maso Gabas, Siddikki, ya ce Fulani sun bai wa Tinubu gudummuwa har ya ci zaɓe
  • A cewarsa, a shirye su ke su karɓi muƙami ko da kuwa masu shara ne a fadar shugaban ƙasa

Mambobin ƙungiyar fulani Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) sun roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tuna da su a wajen raba muƙamai.

'Ya'yan ƙungiyar MACBAN sun bayyana cewa a shirye su ke su yi aiki a matsayin masu shara a fadar shugaban ƙasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
"Mun Shirya Zama Masu Shara a Villa" Miyetti Allah Ta Roki Tinubu Muƙamai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Shugaban kungiyar MACBAN na shiyyar Kudu maso Gabas, Allhaji Gidado Siddikki, ya ce wannan kiran da suka yi zuwa ga shugaba Tinubu ya zama dole.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Uwargidan Shugaba Tinubu Da Mai Dakin Kashim Shettima Sun Sanya Labule Da Buhari a Daura

A cewarsa, fulani makiyaya a fadin kasar nan sun yi addu’a tare da zaben shugaba Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Tribune, Siddikki ya ce:

"Muna neman mukamai daga gwamnatin Tinubu. Ko da a matsayin masu shara a Ofis ne, ba mu damu ba zamu yi. Abin da muke so shi ne mu kasance cikin gwamnatin ƙasa."
“A iya sanina, lokacin zabe, mutanen mu sun zabi shugaba Tinubu ne saboda magabacinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci su zabe shi kuma duk sun yi haka."
“Mun yi addu’a, mun goyi baya, mun amince kuma mun yi duk mai yiwuwa a siyasance don tabbatar da nasararsa. Don haka bai kamata ya mance da mu ba."

Babu bafillatani ko ɗaya a cikin ministoci

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fara Shawo Kan Shugabannin Kwadago a Taron Villa, Bayanai Sun Fito

Ya ƙara da cewa tunda shugaba Tinubu ya fara naɗe-haɗe zuwa yanzu da aka zo kan ministoci, ba bu mamban Miyetti Allah ko guda ɗaya.

“A cikin nade-naden da shugaban kasa ya yi zuwa yanzu, babu wani dan kungiyar Miyetti Allah a ciki, ciki har da wadanda aka tantance a matsayin ministocin da aka nada kwanan nan."
"Bugu da ƙari, batun N8,000 da ake shirin raba wa na tallafin rage zafi da sauran tsare-tsaren da za a amfana na gwamnati, ya kamata a jawo mu a jiki, ko da kuwa a matsayin masu share fadar shugaban ƙasa ne."

Wike Ya Kulla Abota da Jam'iyyar APC Ne Domin Samun Mafaka, Jiga-Jigai a Ribas

A wani labarin na daban Shugabannin APC sun tona asirin tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a daidai lokacin da Tinubu ya naɗa shi minista.

A cewarsu, Wike ya ruga zuwa wurin jam'iyyar APC ne domin ceton siyasarsa wacce alamu suka nuna ta kama hanyar rushewa a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

2023: Daga Ƙarshe, Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Peter Obi Ya Kalubalanci Zaɓen Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262