Rashin Tsaro: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Ribadu Da Hafsoshin Tsaro A Abuja

Rashin Tsaro: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Ribadu Da Hafsoshin Tsaro A Abuja

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu yanzu haka ya na ganawar sirri da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa
  • Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai mai ba da shawara akan harkokin tsaron kasar, Malam Nuhu Ribadu
  • Babban Sifetan 'yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun shima yana daga cikin wadanda suka halarci ganawar

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu yanzu haka ya na ganawar sirri da mai ba da shawara a harkokin tsaron kasa, Mallam Nuhu Ribadu a fadarsa da ke Abuja.

A ganawar har ila yau, akwai dukkan hafsoshin tsaro da shugaban ya nada a ranar 19 ga watan Yuni.

Tiinub na ganawar sirri da hafsoshin tsaro da kuma Ribadu a Abuja.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Legit.ng.
Asali: Twitter

Babban Sifetan 'yan sanda, Kayode Egbetokun shi ma ya halarci taron, cewar gidan talabijin na Channels.

Tinubu na ganawar ne da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Ya Bar Legas Zuwa Abuja Bayan Kammala Hutun Sallah

Daga cikin mahalarta taron akwai shugaban rundunar tsaro, Manjo Janar C. G Musa da shugaban sojin kasar, Manjo Janar T. A Lagbaja sai shugaban sojin ruwa Admiral E. A Ogalla da kuma shugaban sojin sama, AVM H. B Abubakar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun tabbatar da cewa ganawar ba ta rasa nasaba da yadda rashin tsaro ke kara kamari a kasar, cewar Vanguard.

Wannan ganawar ta yau Litinin 3 ga watan Yuli Ita ce ta farko da shugaban ya gana da hafsoshin tsaron da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar.

Ganawar na zuwa ne bayan an nada hafsoshin da kuma Nuhu Ribadu mukamai

Ganawar na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya dawo Abuja daga jihar Lagos a jiya Lahadi 2 ga watan Yuli bayan hutun sallah.

Shugaban a ranar 19 ga watan Yuni ya sallami dukkan hafsoshin tsaro tare da nada sabbin hafsoshin inda ya bukace su da fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Ana So a Kunno Sabon Wuta: An Bukaci Tinubu Ya Ajiye Wike Sannan Ya Nada Wani Shaharren Dan Siyasar Ribas Mukamin Minista

Sallamar ta biyo bayan kiraye-kiraye da ake ta yi wa shugaban akan cire tsoffin hafsoshin tsaron don samun sabbin jini ganin yadda matsalar tsaro ke kara yawa.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Kwankwaso A Fadar Shugaban Kasa

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya na ganawar sirri da jigon jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

Ganawar ba ta rasa nasaba da jita-jitar cewa Tinubu na iya ba wa Kwankwaso mukami a gwamnatinsa.

Kwankwaso na daga cikin 'yan takarar shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel