Babbar Sallah: Peter Obi Ya Zauna da Musulmai, Ya Ba Su Kudi a Gyara Masallatai

Babbar Sallah: Peter Obi Ya Zauna da Musulmai, Ya Ba Su Kudi a Gyara Masallatai

  • Musulman Anambra sun je yawon sallah a gidan Peter Obi domin karfafa hadin-kai da zumunci
  • Duk da cewa shi kirista ne, ‘dan takaran shugaban kasa na LP a zaben 2023 ya yi masu goma ta arziki
  • Obi ya bada kyautar kudi da nufin gyara masallatan da Musulmai su ke yin ibada a Awka da Onitsha

Anambra - Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya yi zama da shugabannin Musulmai a gidansa da ke garin Onitshan jihar Anambra.

Kamar yadda Peter Obi ya yi magana a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, ya gayyaci musulman zuwa gidan na sa ne domin ya taya su murnar babbar sallah.

A nan ya cika alkawarin da ya dauka, na taimaka masu da kudi domin gyaran masallatai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Peter Obi
Peter Obi da Jagororin Musulman Anambra Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

A cewar ‘dan siyasar, makasudin ziyarar ita ce a tunawa ‘Yan Najeriya cewa za a iya hada-kai domin gyara kasar duk da bambancin da ke tsakanin jama’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Obi ya nuna bai kamata sabanin addini, siyasa ko kabilanci ya hana kasar nan samun cigaba ba.

Jawabin Peter Obi

"Dazu nan a yau (Laraba) na karbi bakuncin Musulman Anambra a gidana a Onitsha, domin in taya su murnar bikin babbar sallah.
Sannan na gabatar da takardun cire kudi ga Musulman Onitsha da Akwa domin cika alkawarin da na dauka na gyara masu masallatansu.
Ziyarar dama ce na tuna masu za mu iya magance tulin matsalolin da su ka addabe mu, idan mu ka hada-kai a matsayin al’umma.

Obi: "Dole sai an yi kishin Najeriya"

Tsohon Gwamnan ya karasa jawabinsa a dandalin na Twitter da cewa Najeriya ce kadai kasar da mu ke da ita, dole a dage wajen kawo zaman lafiya da cigaba.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Kafin nan, Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 ya taya daukacin Musulmai murnar bikin babbar sallah da ake yin a Duniya.

Mista Obi ya yi kira na musamman ga Musulami su nuna ‘yanuwa da kishin kasa wajen ibadarsu. An fahimci Obi ya ba su kyautar lemu da buhunan abinci.

Zargin alakar Omo-Agege da LP

Dazu nan mu ke samun labari cewa jagororin APC sun ce Omo-Agege, Peter Obi da ‘Yan Obedient sun kulla yarjejeniya cewa za a goyi bayan Peter Obi a Delta.

An hada-kai domin kada kuri’a ga Obi a zaben shugaban kasa da Omo Agege a zaben Gwamna a jihar Delta a zaben 2023, sai dai a karshe duk su ka sha kashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel