Sallah: 'Haka Zamu Yi Bikin Duk Yadda Ta Zo Mana', 'Yan Najeriya Sun Bayyana Shirin Su Akan Layya

Sallah: 'Haka Zamu Yi Bikin Duk Yadda Ta Zo Mana', 'Yan Najeriya Sun Bayyana Shirin Su Akan Layya

  • Yayin da ake cikin matsin tattalin arziki, wasu mazauna Abuja sun ce sun shirya yin bikin sallah ko ta yaya ta zo musu
  • Farashin dabbobi a kasuwanni daban-daban a Najeriya sai kara hauhawa yake duk da halin da ake ciki
  • Haka a bangaren masu siyar da dabbobin, suma sun koka kan yadda mutane ba sa zuwa siyan dabbobin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Mazauna babban birnin Tarayyar Nigeria, Abuja sun bayyana cewa duk yadda tsadar dabbobi ke kara tashi da sauran kayan masarufi ba zai hana su bikin sallah ba.

Sun bayyana cewa sun shirya don gudanar da bikin sallah duk yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Sallah: 'Yan Najeriya sun koka kan tsadar ragunan layya, sun bayyana shirinsu a ko ya ta zo
Sallah: Farashin Raguna Ya Kara Tashi Ana Daf Da Bikin Salla. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Wani ma'aikacin gwamnati, Abdulrahman Kolawole ya ce shi a bangaren shi zai iya siyan rago amma ya yanke shawarar hadawa da 'yan uwansa don siyan saniya su raba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Abuja: Za Mu Kwace Shanu Mu Kuma Kama Duk Wanda Ke Kiwonsu A Tituna - FCTA

'Yan Najeriya sun bayyana cewa tsadar raguna ba zai hana su bikin sallah ba

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Abu mafi muhimmanci shi ne raba naman ga 'yan uwa da makwabta wanda hakan akwai dumbin lada a ciki idan an yi da zuciya daya.
"Ni da iyalai na muna dokin bikin sallah a kowa ne lokaci saboda muna murna da kuma godiya ga Ubangiji bisa wannan dama.
"Don haka ko farashin raguna ya tashi da sauran kayayyaki dole zamu yi murna da abinda Allah ya hore mana, mun godewa Allah.

Wani dan kasuwa, Alhaji Yawu Mamman ya ce ya dade da siyan kayayyakin da zai yi amfani da su a bikin sallan duk da yanayin tattalin arziki.

Ya ce:

"Na fadawa matana ta siya mana kaji don muyi amfani da shi a sallah.
"A baya na yi yanka, amma yanzu babu hali zamu yi amfani da abin da muke da shi."

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

Masu siyar da raguna sun koka kan rashin ciniki

A daya bangaren, wani mai siyar da raguna, Mista Amos Ayu ya ce mutane ba sa siyan dabbobin saboda tsadar da suka yi, amma ya danganta hakan da matsin tattalin arziki, The Sun ta tattaro.

Ya ce:

"A da, idan zaka dauko rago daga Katsina zuwa Abuja za ka biya N1000 zuwa N1500 amma yanzu sai ka biya N3500 ko babba ko karami.
"Hakanan a baya babban rago ana siyar da shi N100,000 zuwa N150,000 amma yanzu ya kai N250,000 zuwa N350,000."

Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Kyautar Raguna 500

A wani labarin, Sanata Abdulaziz Yari ya rabawa makwabtansa marasa karfi raguna 500 don shagalin sallah.

Shugaban kwamitin rabon ragunan, Alhaji Sha'aya Sarkin Fawa shi ya bayyana sunayen masu karbar ragunan.

Sanatan ya rabawa makwabtan nasa ne da ke karamar hukumar Talata-Mafara da ke jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel