Kungiyar Kwadago NLC Ta Nuna Kin Amincewarta Kan Karin Kudin Lantarki A Najeriya, Ta Bayyana Dalili

Kungiyar Kwadago NLC Ta Nuna Kin Amincewarta Kan Karin Kudin Lantarki A Najeriya, Ta Bayyana Dalili

  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi mahukunta akan shirin kara kudin wutar lantarki a kasar
  • Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni
  • Ya ce karin kudin wutar a irin wannan lokaci bai kamata ba duba da yadda yanayin kasar take

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta soki shirin da ake yi na kara kudin wutar lantarki da kashi 40 a ranar 1 ga watan Yuli.

Kungiyar ta ce yin hakan bai kamata ba a irin wannan lokaci ba, wanda ya nuna rashin kulawa ga kwastomominsu musamman talakawa.

NLC ta yi fatali da shirin kara kudin wutar lantarki da kashi 40
Shugaban Kungiyar NLC, Joe Ajaero. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, cewar Punch.

NLC ta bayyana shirin karin kudin wutar lantarki a rashin dacewa

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

A cewar sanarwar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shirin kara kudin wutar lantarki da kashi 40 da ake shirin yi a ranar 1 ga watan Yuli bai dace ba a wannan lokaci.
"A wannan lokaci, karin ya nuna rashin kulawa ga kwastomomi musamman talakawa.
"Karin ya fayyace yadda aka kara kudin farashin litan mai da kashi 100 wanda ya kawo karin farashin kayayyaki daga kashi 16.9 zuwa 22.1.
"Duk da haka, wannan bai zama dalilin da za a kara kudin wuta ba.
"Duk da haka, ma'aikatar ba ta iya samar da Megawat 5000, sannan akwai kare-karen da aka yi ba tare da sanarwa ba."

Kungiyar ta bayyana rashin tabbas a farashin wutar lantarkin nan gaba

Sanarwar ta kara da cewa kamar yadda Leadership ta tattaro:

"Babbar matsalar shi ne rashin iya gudanar da sabon tsarin inda suka ce zuwa watan Agusta 'yan Najeriya za su iya biyan sabon farashi.

Kara karanta wannan

Biloniya Na Neman Wanda Zai Kular Masa Da Karnukansa Kan Albashi Miliyan N8 Duk Wata

"Daga lokacin da sauran kayayyaki suka tashi, talakawa za su sake shiga wani yanayi."

NLC Ta Rufe Hanyar Shiga Kamfanin ’Yan China Saboda Mutuwar Ma’aikaci Dan Najeriya

A wani labarin, Kungiyar NLC ta rufe hanyar shiga wani kamfanin 'yan China bisa zargin cin mutuncin ma'aikata a Abuja.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda cin zarafin da kamfanin ke yi wa ma'aikata 'yan Najeriya.

Ta bayyana yadda wani direbansu ya rasa ransa saboda rashin ba shi kulawa na magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel