Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

  • Kungiyar Ma'aikata (WAISER) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000
  • Amodu Isiaka, Kwadinetan kungiyar shi ya bayyana haka a ranar Talata 20 ga watan Yuni a cikin wata sanarwa
  • Amodu ya ce dole gwamnatin ta yi dubi akai saboda yanayin yadda farashin kaya ke kara tashi kullum a kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Gamayyar Ma'aikata (WAISER) ta kirayi Gwamnatin Tarayya da ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000.

Kwadinetan kungiyar na kasa, Amodu Isiaka shi ya bayyana haka a ranar Talata 20 ga watan Yuni a wata sanarwa inda ya ce hakan shi zai kawo sauki kan cire tallafin mai da aka yi.

Kungiyar ma'aikata ta bukaci FG ta kara albashi zuwa N200,000
Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

A ranar 29 ga watan Mayu ne dai Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur a kasar, wanda ya jawo wahalhalu ga 'yan kasar, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: TUC Ta Koka Yadda Gwamnoni Da 'Yan Majalisu Ke Sharholiya, Ba Talaka A Ransu, Ta Fadi Bukatunta

Kungiyar ta ce kara mafi karancin albashin ya zama dole

Wannan cire tallafi na da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ya jawo cece-kuce a kasar tare da kiran gwamnati da ta yi abin da ya dace don rage wahalhalun da ake fama da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar NLC da TUC suna ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan yadda mutane ke fama dalilin cire tallafin, cewar Punch.

Yayin gabatar da nata korafin, WAISER ta ce mafi karancin albashi na N30,000 ya yi kadan duba da irin halin da kasar ke ciki inda suka bukaci a kara da kashi 500.

Ta kara neman wasu bukatu bayan karin mafi karancin albashin ma'aikata

Kungiyar har ila yau, ta bukaci gwamnati ta samar da kwanaki biyu a ko wane mako don amfani da harkar gwamnati ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

NAHCON Ta Ce Maniyyata 6,000 Ne Kadai Ba A Yi Jigilarsu Zuwa Saudiyya Ba, Ta Bayyana Dalilai

A cewar kungiyar hakan zai rage radadin cire tallafin da kuma inganta ayyukan ma'aikata.

A cewarsa:

"Ya kamata a kara mafi karancin albashin ma'aikata saboda yadda rayuwa ta sauya da kuma yanayin tattalin arziki a kasar.
"Mafi karancin albashi na N30,000 a yanzu ya yi kadan, muna bukatar kari zuwa N200,000 a wata, kusan karin kashi 500.
"Jihohin Kwara da Edo da sauran jihohi sun samar da dokar hutun kwanaki biyu don saukakawa ma'aikata.
"Jihar Benue ma ta samar da ranar hutu don zuwa gona, haka Jihar Kaduna ma ta samar da hutun kwana guda don ma'aikata."

TUC Ta Ce Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Fadi Bukatunta

A wani labarin, Kungiyar TUC ta roki Gwamnatin Tarayya ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000.

Kungiyar ta ce mafi karancin albashi na N30,000 ya yi kadan duba da yadda komai ya sauya a kasar.

Ta ce duba da hauhawan farashin kayayyaki dole gwamnati ta tabbatar da aiwatar wa da gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel