Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Gintse Aurenta Na Shekaru 14 Da Mijinta, Ta Bayar Da Dalili

Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Gintse Aurenta Na Shekaru 14 Da Mijinta, Ta Bayar Da Dalili

  • Wata mata mai suna Zulai Umar da ke zaune a Gwagwalada, ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta saboda munanan ɗabi'u
  • Matar ta zargi mijin da yawan shan barasa, ta yadda koda yaushe yake kasancewa cikin maye, kuma yana ja ma ta abin kunya
  • Kotu ta nemi jin ta bakin mijin mai suna Umar Abubakar, amma hakan ya ci tura, sabili da a buge yake sakamakon barasar daya ɗinkira

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT - Wata mata mai suna Zulai Umar, ta nemi wata kotu da ke Gwagwalada, da ta raba aurenta na shekaru 14 da mijinta Umar Abubakar, saboda rashin so da ƙauna.

Ta shaidawa kotun cewa shekarunsu 14 kenan a tare, kuma suna zaune ne a Giri Gauta, da ke yankin Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

Wata mata ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta
Mata ta nemi kotu ta raba aurenta na shekaru 14 da mijinta. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Dalilin da yasa matar ta nemi a raba auren

Zulai, wacce ta kasance mahaifiyar yara biyar ce, ta ce wani lokaci a shekarar 2015, ta gano cewa mijin nata yana shan barasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce a lokacin ta yi masa magana kan ya daina shan barasar, amma sai ya ƙi dainawa, ya ci gaba da sha abinsa.

Ta ƙara da cewa, a ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2022, ranar sunan ɗansu na ƙarshe da ta haifa, mijin nata ya shawo giya, yazo cikin maye yana abubuwan da basu dace ba a gaban surukansa.

Zulai ta ce bayan faruwar wannan lamari ne ta tattara yaran ta koma da su zuwa gidan iyayenta, inda ta ce ta shafe watanni goma ba tare da ya waiwayi ko inda suke ba.

A cewarta:

“A wannan lokacin, mijin nawa bai ko leƙo mu domin ya ji ya lafiyar yaransa take ba.”

Kara karanta wannan

Amarya Ta Kai Ango Ƙara Kotu, Ta Nemi a Raba Auren Saboda Yana da Matsalar Ruwan Kwayar Halitta

Da haka ne Zulai Umar ta nemi kotun da ta gintse auren nasu a saboda dalilin rashin so da ƙauna.

Wanda ake ƙara bai ce komai ba kan zargin da ake masa

Ba a samu jin ta bakin mijin nata Abubakar Umar ba, saboda a lokacin yana cikin maye na barasar da ya shawu da ita.

Alƙalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya jawa wanda ake ƙara kunne, kan ya gyara kalaman da yake yi a gaban kotu.

Abdulkarim ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, domin bai wa wanda ake ƙara damar kare kansa, saboda a wannan lokacin, a buge ya zo kotun.

A baya, Eagle Online ta kawo wani rahoto makamancin wannan, inda wata kotun shari'ar Musulunci a Abuja, ta raba auren wata 'yar kasuwa, Rahinat Ahmed, da mijinta Abdulhakim Aliyu, saboda rashin ƙauna a tsakaninsu.

Matar ce ta nemi sakin, inda alƙalin kotun, Malam Ibrahim Rufa'i ya raba auren bayan cika sharuddan da musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa Ta Magantu Kan Kalaman Da Mijinta Ya Yi, Ta Ce Kalaman Ba Gaskiya Ba Ne

Wani magidanci ya fashe da kuka bayan kama matarsa da wani a otal

Wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta yadda wani magidanci ya kama matarsa wacce yake ƙauna da wani gardi a otal.

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a intanet, an ga magidancin na sharɓar kuka a yayinda wasu mutanen ke ƙoƙarin ba shi haƙuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng