Magidanci Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Kama Matarsa Da Gardi a Otal, Bidiyon Ya Yadu

Magidanci Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Kama Matarsa Da Gardi a Otal, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani lokaci ne mai ban takaici ga wani mutumi yayin da ya kama wani mutumi dumu-dumu da matarsa a wani otal
  • Mutumi cike da alhini ya fuskanci matar tasa wacce ba tare da nuna nadama ba game da laifinta ba ta tsaya tsayin daka don kare mutumin da aka ritsata da shi
  • Matakin da mutumin ya dauka bayan nan ya narkar da zukatan 'yan soshiyal midiya yayin da masu amfani da yanar gizo suka mara masa baya gami da tausaya mishi

Wani miji ya fashe da kuka bayan kama matarsa da ya ke matukar kauna da wani mutumi a otel.

Bidiyon da aka gani a TikTok mai karya zuciya ya nuna yadda wani mutumi ya ritsa matarsa a otel yayin da ya fara tuhumarta kan abun da ta ke yi.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba Kabir Ya Ce Ba Za Su Yi Asara Ba, Zai Yi Amfani Da Burbushin Rushe-rushen Don Gyara Ganuwoyin Kano

Bidiyon magidanci ya kama matarsa da gardi a otel
Magidanci Ya Sharbi Kuka Bayan ya Kama Matarsa da Gardi a Otal. Hoto daga @bigdfromthehoosierstate
Asali: TikTok

Ga mamakin mutane, matar ta tsaya tsayin daka don kare mutumin da aka kama ta tana cin amanar mijinta da shi inda ta shiga tsakaninsu.

Mijin ya yi kokarin ganin ya danne zuciyarsa don gudun yin abun da bai dace ba yayin da yayi kururuwa cikin fushi kan cin amanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata mata wacce daga gani ma'aikaciyar otel din ce, ta shiga rikicin inda ta umarci mijin da ya bar harabar.

Yayin bin umarninta, ya ja da baya gami da cigaba da korafi cikin takaici. Daga nan ya fashe da kuka a kafadar wani da ke wurin.

Sai da hakan bai sa matar tasa ta nuna alamun nadama ba.

Martanin 'yan soshiyal midiya

colossal.mind ya ce:

"Na fara zubda masa da hawaye."

MzSnatch Queen ta ce:

Kara karanta wannan

Yadda Aka Ba Hammata Iska Tsakanin Jami’in NSCDC Da Dan Bautar Kasa a Kan Abinci

"Da gaske ina masa kuka ina ji masa radadi."

MookieVaporLock ta ce:

"Na fuskanci irin haka shekaru biyu da suka shude. Cikina na kadawa sosai duk lokacin da na tuna da cin amanar."

Romii ta ce:

"Naji wa wannan 'dan uwan takaici... yana da sauki a ce an manta da komai sai dai idan da kai ya ke faruwa. Lokaci zai warkar da shi."

harlan64 ta ce:

"Duk da haka sai da ta shiga wannan dakin. Na fuskanci hakan a farkon rayuwata, hakan abu ne mai ban takaici."

Williams ya ce:

"Kuma har ma kare kwarton nata ta ke. Yanzu idan da ya juya ma ta baya bai waiwaya ba ta yi asara."

Mon b ta ce:

"Mutumin nan ba rago bane..abun ya bata masa rai... ba zai taba yarda da wata mata ba...ku yarda da ni."

Mrs B ta ce:

Kara karanta wannan

Maganin barna: Uwa ta cije, ta hana danta jakar makaranta, ta mika masa buhun siminti

"Lokacin da ta rungumi dayan mutumin naji ma mutumin haushi, amma zai samu wacce ta fi ta."

'Yan mata biyu sun ba hammata iska bayan kowacce ta shiryawa saurayi bazday

A wani labari na daban, wata budurwa ta labarta irin mugun damben da suka ci da wata a gidan saurayinta ranar da ta shirya masa bazday.

Ta je da masu algaita amma cike da abun mamaki ta tarar da wata ta shirya masa shagali ita ma, tuni aka ba hammata iska.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel